chapter 40

1.8K 124 7
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

*****
  Baki sake hajjo ke kallo miemie,batagama dawowa daga mamakinta ba miemie tacigaba da cewa.
"Do not judge a book by it's cover Karki fassara mutum daga fuska,suffa ko kuma shiga saboda bakisan tsakanin mutum da mahaliccin sa ba,imani da tsoron allah a zuciya yake,kuma halayya ko shiga bazaisa ki k'ira mutum da d'an aljanna ba saboda watak'ila akwai sa6on da yakeyi a 6oye ke baki saniba allah ne kurum yasan zuciyar mutum."ta k'arishe tana kallonta.
Yanayinta ya nuna ranta yakai k'ololuwa a 6aci, hatta yaran cikinta babu Wanda ya isa ya gayamata magana irin haka.
Su kansu su zarah alamunsu ya sun tsorita suna jiran matakin da hajjo zata d'auka.
"Get out."tafad'a angrily. 
Baki galala miemie ke kallonta.
"Karki kuskura na bud'e Ido naganki anan."
"But...
"I said out."ta daka mata tsawa ba shiri miemie ta mik'e tsaye tana kallonta, bata daddara ba tace.
"I'm sorry in maganganun Dana fad'a sun 6ata miki rai,but gaskiya na fad'a kuma zan dad'a maimatawa duk sanda kika suffantani da kafirai, amma kiyi hak'uri."
Cikeda 6acin rai hajjo ta mik'e tareda nuna mata k'ofa.
"Duk da ansanar dake dokokin gidan nan nakejin babu Wanda ya shiga k'wak'walwarki, tun zuwanki nake maimaita miki ki iya bakinki wajen shiga abunda bai shafeki ba,koda yake ba laifinki bane I made a very huge mistake da  tun farko wajen gayyatan marar hankali nan gun,duk da sanin halayenki na rashin sanin mutunci da kuma girmama mutane baisa na daddara ba,kibud'e kunnuwanki kijini dakyau ki tsaya a matsayinki, bar ganin na kyaleki aduk abubuwan dakika aekata zuwanki nayi hakan ne saboda ganin mutuncin ki amma   ke baki kama naki mutuncin ba balle har wani ya gani, wannan ya zama rana na k'arshe da zan ganki a kusa dani,duk inda kika ganni tun kafin na ganki ki canza hanya,dan kika kuskura na ganki a ranar zan nuna miki iyakarki...get out!"tafad'a tana nuna mata hanya.
"She's going no where..."suka tsinkayi murya daga entrance.
Atare suka kalli shi tsaye fuskarshi nanan yadda yake babu walwala, sanye yake da navy blue suit da white shirt sai tie nasa navy blue bai bai d'aura da kyau ba, gashin kansa sai shek'i yake, k'amshin turarensa ya mamaye ko ina.
Miemie dake tsaye cikeda 6acin rai jin furucin hajjo, _EMPEROR_ ta furta a hankali ganin PMB yasa ta kasa d'auke ido a akanshi, zuba mata glassy grey eyes nasa yayi hakan yasa tsoron jiya ya dawo sabuwa fil dasauri ta d'auke idanunta daga kanshi,cikeda mamaki hajjo ke dubansa.
"Murad...
"Yes umma,she's going no where saboda banga laifin data miki ba."yabata amsa kai tsaye tareda Jan kujerar opposite da miemie gefen amatullah ya zauna tareda jawo fruit salad bowl dake gabansa.
"Murad wani kake gayawa maganar banza,tun yaushe kafara mayar mun da magana har wata tayimun rashin kunya kana kabi bayanta."
Ajiye bowl d'in yayi ba tareda ya dubeta ba ya rik'o hannunta tareda zaunar da ita, d'aga glassy grey eyes nasa yayi ya sauk'e akan miemie data kasa d'auke idanu akansa,komai nasa da isa yakeyi,dasauri ta sauk'e idanunta dan idanunsa tsoro yake bata.alama yai mata da hannu data zauna,babu musu kamar wacce k'wai yafashewa a ciki ta zauna.
Tura bowl d'in fruit salad d'in yayi bayan ya jefa ice zuwa gaban hajjo.
  Mai martaba kallonsu kawai yakeyi yana sak'a wash abubuwa aranshi fuskarsa d'auke da murmushi.
Murad ya dubi hajjo yai mata alama da hannu ta sha.
Harara ta banka masa.
"Murad nafad'a maka kafita idona, meka maidani? Kakarka? Wai ni tsaya, tun yaushe kafara gayamun magana gatsatsau haka, na lura kwana biyu akwai abunda ke damunka, wato rainin naka ya dawo kaina, har wuyanka yayi kaurin da baka bin umarnina, duk abunda nace kanada amsar bani, kwata kwata kadaina girmamani,yau ko idanunka bangani da asuba ba, 'yan uwanka duka sunzo sun gaisheni kai meya hanaka zuwa, kagayamun ko ka canza wata uwarne?"tafad'a fuska a tamke.
Tunda ta fara harta gama PMB baidaina kai spoon baki ba, hankalinsa naga abunda ke gabansa, fuskarsa kamar ko yaushe expressionless,amma a zahirin gaskiya maganganunta na shigarshi, saida ta gama yadubi zarah.
"Why are you still not eating? Tashi kisawa abba abinci."yafad'a batareda ya dubi inda mahaifiyar tasa ke zaune ba.
Kallon inda miemie take yayi,had'a idanu sukayi ya mata wani mugun kallo, da Sauri ta d'auke kai tana kallon gefe.
Zarah da amatullah sukayi serving gaba d'aya banda miemie dake zaune sukuku.
  A tare suka karanta addu'ar cin abinci kafun kowa yafara cin nasa, hakan ba k'aramin burge miemie yayiba, ita a gida kowa aransa yakeyi Wanda itakam wataran ba yi takeyiba.
  "Murad bada...
  "Umma please... At least eat your food first."yafad'a kai tsaye bayan yad'an dubeta.
Miemie na zaune sukuku takasa d'auke idanunta daga kan PMB, komai nasa burgeta yakeyi daga jiya zuwa yau,bata ta6a jin wani ya burgeta ba daga namiji har mace sai akan PMB, musamman yadda yabi bayanta akan hajjo, that means duk abunda yafaru a idonsa ne,komai nasa a hankali yakeyi cikin kwanciyar hankali, k'iris ya rage su had'a Ido tayi maza ta sauk'e.
_what the heck is wrong with me? Why am I very nervous all of a sudden?_ tafad'a a ranta bayan ta runtsa Ido.
"Mariam are you okay?"ta tsinkayi muryar mai martaba yana mata murmushi.
Murmushin Yak'e tasake da sauri.
"O.. Eh... Yes am fine."tafad'a muryarta na rawa tareda duban direction d'in da hajjo da murad suke, hankalinsa naga cin abincinsa ko kallo bata isheshiba,hajjo kua wani kallo ta watsa mata data kasa gane manufarshi.
"Why are you not eating,Serve yourself please."Cewar mai martaba.
Ahankali kamar mai tsoron wani abu ,gaba d'aya taji yunwar ma ya tafi, chips da scramble egg ta d'eba tareda had'a tea gaba d'aya She's uncomfortable Karo na farko a rayuwarta.
Tana fara ci folk nata yafara k'ara a plate d'in, duka suka d'ago suna kallonta dan k'arar ya wuce misali,gaba d'aya batada tables manner.
D'agowa tayi ta dubesu caraf suka had'a Ido da PMB.
"I'm sorry."tafurta cikeda kunyar yanayin cin abincinta Karo na farko a rayuwar ta.
  Kasa controlling folk nata tayi gaba d'aya tafara jin haushin kanta, sabo ne Wanda ya riga yabi jininta, kullum mama saitayi mata fad'a amma saita shararantar, Yau gashi taji kunyar kanta tarasa dalili, duk kalan ci na miemie ranar kasaci tayi saboda wani yanayi data tsinci kanta.
   Suna cikin tsakiyar cin abinci amatullah tayi gyaran murya, a tsorace ta dubi hajjo dake cin abinci fuskarta a had'e.
"Um... Umma ina
D'agowa tayi tadubeta Wanda ya dad'a tsoritar da amatullah.
Runtsa Ido tayi tareda cewa.
"Umma dama maganan...
"Amatullah karki k'ara 6atamun rai, I've already made up my mind, is either kiyi abunda nace ko kifasa makarantar, in har na isa dake saidai in zaki bujiremu kamar 'yar uwarki."
"Umma but ae ba field d'ina bane, Dan allah umma kar..."
"Karki 6ata bakinki saboda bazaki canzamun ra'ayiba, Dole kiyi abunda nakeso in ni na haifeki.
Hawayene ya zubo mata tana kallon hajjo cikeda tausayin kanta, su kenan basuyi deciding Abu a rayuwarsu ba sai abunda hajjo tace.
Tashi tayi zata bar gun hajjo ta daka mata tsawa.
"Zauna."
Ba shiri ta zauna har tana neman fad'uwa sanda zarah ta tareta.
"Wannan yazama na k'arshe da zan miki magana kinemi tashi agun."tafad'a tareda banka mata harara.
Kallon zarah tayi hawaye fal a idonsu duka biyu, girgiza mata kai tayi alamar tayi shiru.
Zarah ta dubi hajjo.
"Umma dan allah ina buk'atar wayata nad'an lokaci kad'an..."
"Karki kuskura ki kawomun zancen banza anan,inajin na fad'a miki keda rik'e waya saidai mijinki ya saya miki..."
Shiru tayi bata kuma cewa komaiba.
Miemie kallonsu take cikeda mamaki,haka kurum taji tausayin su zarah,wannan wace irin uwace ji yadda take treating 'ya'yanta tamkar ba ita ta haifesu ba,tasan duk rashin jin maganar ta mama bata ta6a mata abunda hajjo kewa 'ya'yanta,tunda har sukaji tsoron mahaifiyarsu akwai matsala.
Kallo mai martaba tayi taga ko a jikinsa cin abincinsa yake,maida kallonta tayi kan PMB shima ko kallo basu isheshi ba,nazari tafara sosae a kansu.
Mik'ewar PMB ne yasa tadawo hankalinta.
Hajjo tadubeshi tace.
"Ina kake tunanin zuwa bamu gama magana ba."
Lumshe idanunsa yayi Wanda a iya zaman da miemie tayi ta lura shine al'adarsa.
  Duba agogon hannunsa yayi kafun yadubeta.
"Am running out of time..."
"Baka fad'amun inda zaka ba."tafad'a tana dubansa.
"Meyasa kike maidani tamkar yaro k'arimi,am not a kid anymore kinsan bazan kai kaina inda bai kamata ba."yafad'a dukda fuskarsa bai nuna alamun 6acin raiba husky voice nasa ya nuna.
"Ooo... I can see wuyanka yayi kauri murad, kanasa inafara kokonto anya baka fara shan Abu ba."
"What? You're unpredictable umma...Inaga I'll be better off idan nabar nan gun."yafad'a tareda d'aukar coat nasa zai fita Wanda 6acin rai k'arara ya nuna a fuskarsa.
"Murad..."ta k'irasa muryarta alamar karaya.
Tsayawa yayi batareda ya juyoba.
"Idan kadawo inada magana dakai."
Juyowa yayi ya dubeta.
"Bakida maganar dazaki fad'amun bayan Wanda kika fad'a d'azu,kafun ki k'ara nemana sai kin tabbatar da asalin d'anki, dan haryanzu na lura akwai sauran kokontonki akaina dakuma halayyata."yana kaiwa nan ya juya ya fita.
Zarah da amatullah sukabi bayanshi.
Ahankali miemie ta mik'e abubuwa dayawa sak'e a ranta, ta gefen hajjo dake tsaye sukuku ta zo wucewa taji hajjo tace.
"Kar abunda kika gani yasa rashin kunyarki ya k'aru, murad d'anane kuma ina iya tank'warashi duk yadda naso kar amsar daya bani ya k'ara miki k'arfin gwiwa dan haka ki tattara sauran ki Adana harsaikin bar gidannan."
Miemie batayi maganaba tasakai tafita gaba d'aya kanta a d'aure,dan bawani jin maganganun hajjo tayiba.
  Shiru hajjo tayi bayan ta zauna tareda dafe kanta tana tuno abunda yafaru a yanzu, wash hawayene masu zafin gaske ya zubo mata Wanda ita kad'ai tasan manufarsa.
Mai marbata ya dubeta.
"Khadeeja Karkice komai, ina respecting decisions naki a kullum kuma banta6a miki shisshigi akan abunda kika yankeba, kodan wannan Karo na farko zansu ki respecting nawa decision d'in.Nasa a bata d'akin marigayi safwan sannan nace tare zamuna cin abinci saboda na nuna muku cewa Mariam is also part of this family tunda a gaban iyayenta nasa aka d'auko ta,itama tana k'ima a idona kamar su zarah, kema zansu kibata matsayin 'yarki.kamar yadda nafad'a miki jiya yau zan maimaita ban yarda wani yaci mata fuska koya wulak'an tata ba,sannan ko kad'an banji haushin abunda ta fad'a miki ba saboda gaskiyace kuma duk nan munsan da ita kikeyi, karki d'auka dan rashin kunya ta fad'i hakan, aah ita haka take gaskiyar abunda ke zuciyan take fad'a, kuma komai 6acin ran da zaki shiga bazaisa tak'i maimaitawa ba, ba goyon bayanta nakeba amma zanso kema kigyara magan ganunki gaba."yana kaiwa nan ya dakata.
  Runtse Ido hajjo tayi tanajin wani d'aci a zuciyarta.
"Allah ya huci zuciyarka insha allah za'a gyara."tafad'a tana kallonsa.

*****
  Bayan fitowar miemie tanufi hanyar d'akinta gaba d'aya brain nata baya functioning sosae, yanzu haka zata rayu a cikin gidan nan, ita komai ya isheta tundaga yanzu.
IPad nata ne ya fad'o mata, yanzu take buk'atarshi saboda video call da mutanen gidansu, ya zatayi kenan? Ita harga allah emperor tsoro yake bata.
Dab zata shiga d'aki shima yafito all dressed up.
Cak ta tsaya tana kallonshi,kamar baisan da tsayuwar mutum agun ba yasa kai ya wuce.
Cizan yatsa miemie tafara yazama lallai ta tambayeshi. Runtse Ido tayi _c'mon miemie you've to be your real self, fearless miemie_ take taji wani k'arfin gwiwa.
Da k'arfi tace.
" *Emperor*"yadda zai jita.

******
_anya babu wani 6oyayyen al'amari dangane da wannan gidan?_
_anya da gayya hajjo ke yiwa 'ya'yan cikinta haka?_
_anya miemie zata iya cigaba da zama a wannan gidan?_
_anya miemie zata iya yiwa PMB maganar dubaga yadda take tsoronshi?_
_to nima dai bansani ba mucigaba da zuwa_🏃🏽‍♀🏃🏽‍♀🏃🏽‍♀

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang