"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly.
"Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried
"No...
***** Tunda suka d'au hanya miemie kejan driver ManSadi da hira tuntana tambayar abu mai ma'ana hartafara na shirme, shikuwa sai biyemata yakeyi, nan danan suka saba sai labari suke baiwa juna angamu da andace da suka gaji kowa yayi shiru...itakuwa ganin haka yasa ta d'an kyaleshi tasanya headphone a kunnenta,kasancewar bawani tafiya bane Mai nisa around k'arfe hud'u suka iso. Ware idanu tayi tana kallon cikin gombe, sun d'anyi tafiya mai tsawo kana suka Iso gate d'in palace, d'aga kai sosae tayi tana kallon ginin tamkar ba'a Nigeria ba,nan kuwa tahau wasu tamboyiyin,duk surutun bawan allah'n nan saida ya sarawa miemie. Securities ne kota ina, titine shimfed'e ko'ina a cikin fad'an,tafiya sukayi na kusan minti sha biyar kafun suka iso main gate na shiga cikin masarautar, baki bud'e miemie ke kalle kalle tunda take a rayuwarta bata ta6a kallon gini irin hakaba dan sosae ya k'ayatu,gine ginen gargajiya,dawakao da sauransu, mamakine ya kamata ganin instead of su shiga wannan gate d'in zuwa asalin cikin fada saitaga ya juya akalar motar zuwa titin dama,kasa hak'uri tayi tadubi driver'n. "Amm ManSadi ince wancan gate d'inne destination d'inmu?" "A'ah hajiya dasauran tafiya." "Da sauran tafiya?" Ta tambaya curiously "Eh Dr, ba cikin asalin masarautar zamuba... "Kozan iya sanin dalili?" Ta katsesa. "Ehtoh! Mai martaba bai cikin asalin fada yana wani shashi daga cikin masarautar."yabata amsa a tak'aice. Mamakine ya kama miemie tanason yin tambaya taji muryar mallam sadi. "Tun farin rashin lafiyar mai martaba yabaro can yadawo nan shida iyalansa..." "Amma meyasa mai martaba yabaro cikin asalin fadarsa zuwa wani gu daban?" "Shidakansa ya buk'aci hakan acewarsa yanaso ya nisanci al'amuran mulki zuwa wani lokaci kafun allah yasa ya samu lafiya." D'an jim miemie tayi nad'an wani lokaci kana tace. "Wake mulkin a yanzu? Kokuwa a cikin 'ya'yan sa wani ya maye gurbi?" D'an dariya kad'an sadi yayi kana yace. "Mai maitaba baiyi murabusba,ya damk'awa hakimi komai a hannunsa kafun Allah ya bashi lafiya." "Baida magada ne?"miemie ta jefo masa tambaya kai tsaye. Jimm yayi kana cikin damuwa yace. "magadan mai martaba sunkai biyar amma a halin yanzu d'ayane a raye kuma shi baida ra'ayin sarauta ko kad'an." Miemie batasake magana ba taja bakinta tayi shiru,tambayoyine fal a ranta amma asannu zata gane komai. Wani tambatsetsen gate suka nufa take sadi ya nausa horn...wani soldier ne yafito saida ya tabbatar sananne ne kana ya wangale gate d'in, baki miemie ta bud'e tana kallon mansion d'in gabanta, babban gidane sosae wanda yayi shege da ginin sarauta amma ginin zamani hawa uku, filin gidanma abun kallone sosae ya k'awatu.Ana parking miemie ta fito tana dariya.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
"Wow!" Ta furta dagudu takwasa tayi tsakiyar wani makeken garden ta kwanta a k'asa tareda lumshe idanu. "Here I am! In the royal mansion woooh!"tasanya ihu tareda ciro wayanta ta fara d'aukar selfie. Mallam sadi ne yafito da akwatinta kana ya dubi ya k'arisa inda take yana dariya dama yasan hakan zata faro. "Bismillah likita, muk'arisa gurin sarkin gida." Mik'ewa tayi tsaye tana karkad'a jiki tana dariya tabi bayanshi tana waige waige, ma'aikatane sanye da unifoam ta ko'ina kowa na aekin gabanshi, securities na gaba d'aya sojojine rik'e da bindiga suna tsaye kyam kamar statues. Tadubi sadi tace "ManSadi meya kawo soldiers nan kuma? Nasha gidan sarauta fadawa ke kula da komai, sannan kuma banga alamar akwai abubuwan gargijiya yana gudana anan ba irin busa algaita da sauransu." "A ra'ayin 'yan gidan nan basa buk'atar haka... Yareema ne ya dakatar da komai, anan gidan ba fadawa ba kuyangu dasauran ma'aikatan fada, hatta masu kula da dawakai sojojine, 'yan aeki mata daga nesa aka kawosu, mahaifina shine sarkin gida kuma shine amintaccen bawan sarki, sannan nine amintaccen bawan yareema, bayan gamu anan babu Wanda yasan sirrin gidannan." Karo na biyu jin an ambaci yareema k'irjinta ya bugs sannan ga Mamakine k'arara ya bayyana kan fuskarta, toshi wannan yareeman wani iron mutunne, meyasa ra'ayinsa yayi daman dana mutane, wasu sunanso su gansu cikin wannan daulan amma ya samu haryana watsi da damarsa, ita so kawai take taga wannan mutumin. Daidai lokacin dasuka Iso k'ofa, bayan anbud'e musu yadubeta yaimata alamar tashigo da hannu, shikuma yaja akwatinta yana gaba tana baya, wani dog on corridor tagani Wanda bata iya hangen k'arshensa,bayan sun wuce k'ofof'i uku na hud'unne suka shiga,wani d'an madaidaicin falone dayasha kayan alatu,saiwani tashin k'amshi yakeyi take miemie ido ya raina fata,wangame baki tayi tana k'auyanci dakyau. "Bismillah zauna bari na k'ira sarkin gida." Ta tsinkayi muryar ManSadi. Jinjina kai tayi kana ta zauna tareda ciro waya tahau d'aukar selfie,dataga zaman bazaiyiba ta mik'e komai tasamu saita d'auki hoto a gurin. Dab da k'ofa tazo ta hangi wani abu kamar statue sanye da kayan yak'i ji tayi ya burgeta,k'arisawa gun tayi tareda ta6awa,garin gigil gigil d'inta ta ture take abun ya girgiza tamkar zai fad'i,k'ok'arin tarowa takeyi taji nauyin abun yawuce tunaninta sai nishi take,ji tayi ansanya hannu a tura,waro ido tayi dan ita kawai gani tayi abun ya koma normal state nashi,juyawa tayi da saurin dan ganin wa ya taimaketa sai ganin wani d'an dattijo tayi wankan tarwad'a murmushi d'auke a fuskarshi yana sanye da manyan kaya da rawani d'aure a kansa,koba'a fad'aba tasan shine sarkin gida mahaifin ManSadi Dan yanayin dasukeyi, Murmushin yak'e ta mayar masa na ba shiri Dan mutumin ya mata k'warjini. "Dr. Anas, Mariam Anas!" Tafad'a zealously tareda mik'a masa hannu. Batareda ya mayar mataba ya wuce tare da cewa. "Bismillah Dr. Anas"tareda nuna mata kujera. Gaishesa miemie tayi saboda tuna jaddadawan mama gurin gaisuwa, da fara'arsa ya amsa. Jiki na rawa tasamu inda ya nuna mata ta zauna, take akacika mata gaba da kayan mak'ulashe. Ta dubi yarinyar data kawo mata a k'alla zatakai shekaru ashirin da uku. "Thank you!" Tafad'a cheerily Nodding kai kurum yarinyar tayi tana murmushi. SG yace. "Mermu ki isar da sak'ona gurin Tani kice ina son ganinta da gaggawa." Bayan fitar mermu SG yadubi miemie datasa snacks a gaba tanaci tsakaninta da allah ko d'an bak'unta babu. "Sannu da zua fadan Abdulazeez Bayero,munji dad'i matuk'a dakika amsa gayyatarmu." Murmushi tayi kurum tana cusa nakiya a baki. "It's my pleasure!" Tabashi amsa da Abu a bakinta. Murmushi yayi danji yayi yarinyar ta shiga ranshi, dukda batada wani shekaru amma yana ganin zata musu abunda sukeso. Gyaran murya yayi ya dubi miemie. "Dr Anas da farko muna mai godiya dakika bamu had'in kai na zuwa Nan fadan domin zuwanki yanada matuk'ar amfani garemu dama alumma gaba d'aya, ina so kibani aron hankalinki domin sauraron abunda zan fad'a." Nutsuwa miemie tayi tareda ajiye glass cup d'in dake hannunta tabashi full attention. "Ina sauraronka!" "Dr.Anas Akwai wani Abu damuka gani tattare dake wanda acikin wannan nahiyar tamu ta yanzu zaiyi wuya a samu mutum musamman mace irinki, nasan zakiyi mamaki dajin hakan,amma bamu nemikiba sands muka yi doguwar bincike akanki kama daga gidan dakika fito, yanayin rayuwarki,al'amuranki da mutane uwa uba kuma sanin kan aekinki, Likitoci irinki sunfi goma Wanda sukazo wannan masarautan amma allah baiyi sune sanadin warkewar ma marbataba dalili kuwa shine baibasu had'in kai gurin aekinsu,na biyu kuma basa maida hankali sosae kan abunda ya kawosu abunda nake nufi shine son abun duniya ya rufemusu Ido, bazaki fahimci abunda nake nufi da hakanba yanzu sai zuwa gaba, mai martaba yariga ya fidda rai ga samun lafiya Wanda har yake tunanin shine ajalinshi, yana cikin mayuwacin hali Wanda allah ne kawai zai iya bashi lafiya,saiyasa muka zage wajen ganin munsamamar masa da lafiya koda kuwa mak'iyansa basaso,Dr.Anas a halin yanzu da taimakon allah ke kad'aine zaki iya samarwa mai martaba lafiya." Kan miemie gaba d'aya ya d'aure me yake nufi da maganganunsa. "Tayaya kake ganin ni kad'ai zan iya Samar masa lafiya bayan irina dayawa sun kasa..." Bata k'arisaba ya katseta. "Saboda akwai abubuwan al'ajabi game dake, there are some special things about you Wanda ke bazaki ganiba, Dr. Mariam gidan sarauta ya wuce tunaninki saboda akwai mutane daban daban a cikinta, bazaka iya ganin abunda ke cikin zuciyoyin mutaneba, barin fito miki yadda zaki gane, masarautar nan tana d'auke da mutanen dabaki tsammani akwai irinsu a duniya, son kai, son abin duniya, mugunta, ha'inci, munafurci dasauransu babu Wanda babu, a saninki damukayi kece kad'ai zak'i iya taimaka mana amma saikinyi taka tsantsan, bawai munjawo ki cikin hatsari bane a'ah, akwai tsaro da komai amma kema sai kin zage naki damtsen, ko kad'an bamu d'aukokin gaban iyayenki dan mujaki cikin hatsari ba, taimako zakimana dan Allah kuma shi kad'ai zai iya biyanki, magana tak'arshe shine mai kama da gargad'i KAR SHIGA ABUNDA BAI GAMEKI BA, SANNAN KAR KI YARDA DA KOWA, kiyi focusing kan abunda ya kawoki...sannan gameda mutanen gidannan karkiyi stressing kanki wajen shiga hark'arsu,kowa da kalan halinsa kama daga uwar gidan sarki zuwa yaran gidan,dan wani irin rayuwa akeyi na bamai shiga hark'ar wani kowa hark'ar gabansa yake,tun farin rashin lafiyan mai martaba gidannan yakoma wani iri na rashin zaman dad'i da walwala,kowa cikin bak'in ciki yake,zaki fuskanci wulak'anci amma wannan bashine a gabanki ba,kiyi aekin dayakawoki batare da kin shiga hark'ar kowaba musamman YAREEMAH MURAD" Bai idasa ba sukaji sallamar mace. Murmushi ya mata kana yace. "Shine kawai, abunda zan iya ce miki, allah yasa a samu abunda ake nema." Miemie dai na zaune kamar statue kanta gaba d'aya ya since, meyasa suke ganin ita zata iya abunda wasu suka kasa, meke camera ita dasuke ganin ita kad'ai zata iya ku6utar da mai martaba, allahu aalamu,wani irin zama kenan akeyi a gidannan. Bayan shigowar Tani SG yace "Tani ga sabuwar likitan mai martaba, mermu tana kula da ita sosae, sannan yanzu ki kaita gurin uwar gida dan tasan da zuwanta sannan a wuce da ita masauk'i. "Toh yalla6ai." Cewar Tani. SG yadubi miemie "Dr. Anas kibita zuwa gaida uwar gidan mai martaba sannan duk wani abunda ya shige miki duhu ko kike buk'ata kiyi gaggawan sanar dani yanzu bari a kaiki masauk'i ki huta zuwa safiya zaki fara aekinki." Nodding kai kurum miemie tayi tareda mik'ewa tani taja akwatin ta suka fice gaba d'aya kan miemie a k'ulle. Tafiya sukayi mai tsawo tani na gaba tana binta a baya, sai kalle kalle take tana mamakin had'uwar gurin. Wani had'adden makeken falo suka shiga Wanda yaji kayan alatu, duk irin yawon da miemie tayi k'asa k'asa bata ta6a ganin falo had'add'e irinshi ba, gaba d'aya ta kasa 6oye k'auyancinta. Muryar tani ce ta dawo da ita. "Barina sanar da HAJJOH" Miemie sai kalle kalle takeyi.
******** Tohfah! GAMIEMIE A MASARAUTARABDULAZEEZBAYERO,Nima kainayak'ulle. Menene a cikinwannanbabbangidan Wanda sarkingidakecewamiemiecekurumzataiyawarkar da mai martaba? Shin wanihaliiyalan mai maryabasukeyi Wanda miemiebazataiya zama dasuba? Shin waniabunal'ahabinegameda PRINCE MURADBAYERO?