chapter 16

1.9K 123 2
                                    


In dedication to
miemiebee👄

There's no sophistication in my lack of patience,I'm just wishing you were better at communication,as I sit here steady waiting,wishing that you would call my name in,wishing I was better with distance,it's cause you're the only one I'm really missing,nobody would be forgiving,cause of all the love that you gave me.

~Strong~

*~*~*~

Da yamma ammar da miemie na hanyar dawowansu daga islamiyya da k'afa kasancewar babu nisa sosae tsakanin makarantar da gidan hajja,sai cakalar mutane fad'a sukeyi,su zagi wancan su jefi wannan da dutse duk babu mai kulasu kasancewar ansan halinsu kana magana yanzu su lakad'a maka na jaki su falfale kuma babu wanda ya isa yakaiwa hajja k'ara Dan yanzu zata tsigaleka tace jikokinta basa calakalar fad'a saidai in an ta6osu su rama.

Tafiya suke miemie nashan alawa tana lashe hannu saiji tayi ammar ya buge mata shoulder alewar ta tafad'i.

"Kutumelesu! Kayar__"

"Ke dallah rufamun baki Abu nake nuna mini."

"A haba!"

Direction din takalla,wani saurayine da budurwa suna zance suna tafiya kasancewar ba sosae suke kallonsu ba dan tsabaragen gulma batasan ta hankad'e mutum ba juyowa tsohon yayi yana kallonta

"Ank'i ace sannun." Tafad'a tareda bankamai harara.Girgiza kai kurum yayi ya wuce.

"Ke kin ganeta?"
"Niko naganeta! Ba safara bace Mai aekin ummi?"

"Iyee!"

"Fav twin mik'omin dutsen can yau saina rama bugeni datayi ranan."

Tattaro duwatsu yayi yamik'a,daidai saitin d'uwawunta miemie ta saita tareda wurga mata dutsen dasauri suka juya kamar basuba.

"Washh" tace

Saurayi yace "Lafiya dear ko kingaji ne?"

Murmushi ta k'ak'alo tace "Eh nagaji da tafiyarne kurum washhhh." Tasake jin dutse a d'uwawunta.

"Kodai bakyajin dad'ine?" Saurayin yakuma tambaya cikeda damuwa
Murmushin takuma yi tace "A'ah taf... Washhh!" Wannan Karon k'ara tsake dan bak'aramin shigarta yayi ba.

"Ko cikin ki ke ciwo mu zauna kafunnan?"

"A'ah wahhhhhhh!"Atare suka juya sai hango ammar da miemie sukayi har sun kai k'asa dan tsabar dariyan mugunta.

Saurayin ransa yamugun 6aci yanufi gunsu,atake suka kwasa a 360.

~*~*

Bayan sun d'an k'ara gaba suka d'an dakata suna haki had'eda dariya.

"Fav twin ke muguwace wallahi"

"Kace mu mugayene naga tare muke jifan."

"Ke that's by the way Allah abu nakeson ci mai dad'i"

"Dalla matsacan munafuki bakai kayarmun da alawa naba."

"Naga ae abu na nuna miki lokacin har yakai ki yin wannan dariyar."Yafad'a yana harararta.

"Eh dai naji ae gashi yanzu ka mana asara."

"Ke na hango abu" Yafad'a joyfully

"A ina? Mehne?" Tafad'a tana lek'a inda yake kallo.

Wani leda suka hango Saman wani guntun katanga."Aradu naji k'amshi kamar Ana soya tasoyu."

"Kinga yanzu aka wurgo k'ila tasoyunne tamak'ale saman katangar."Cewar ammar

"Yaya kenan?" Miemie ta tambaya

"Ya wuce mu d'auko mu duba."

"Chabdi! Tayaya tsayinmu zaikai wannar katangar?" Miemie ta tambaya tana harararshi.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now