chapter 82

1.5K 156 5
                                        

In dedication to
Miemieb
 
******
  Hankalin Hydar yafara tashin ganin ya kira layin maheer uncountable times amma bai d'auka ba.
Kutsawa yayi cikin dandazon mutane ya tsuguna tsakankanun baba da abba yace.
"Abba na kira layinsa bai d'aga ba inaga zanje gida nadubo no lafiya dan bai ta6a hakanba."
  Shikansa abban yasha jinin jikinsa dan da mamaki ace har yanzu maheer bai isoba.
Baba yadubi abba yace
"Meya hanaku tahowa tare tun fari?"
"Yace nafara gaba zasu taho tareda khaleel, amma sai ganin khaleel nayi yazo shi kadai Dana tambayesa ina maheer yace yasha muntaho tare dan ko kiransa baiyiba."yakarishd sounding worried
"Allah sa dai lafiya, kai da khaleel kuje maza ku duboshi."cewar Abba
"Meye kuma abun sai yazo Alhaji, tunda sadaki na hannu mai zai hana a daura kawai."
  Abba ya girgiza kai yace
"Ba'ayi haka ba Alhaji... Bamusan meye dalilin rashin zuwan yaro ba.... Tunda akwai daurin auruka gaba a daura kawai kafun hydar din yadubo maheer din."
Duk yadda baba yaso a daura auren a lokacin abba ya kiya acewarsa sai anga lafiyan maheer din daga karshe babu yadda baba ya iya hakan yasa aka cigaba da wasu daurin auren.
  Hydar na banyan zuwa gida shida khaleel har alokacin bai daina trying numbern maheer ba, a yanzu hankalinsa yafara tashi dan maheer bai ta6a yin hakan ba.
  Tun kafun khaleel yayi parking hydar ya bude kofar motar saura kiris ya bai damuba burinsa kurum ya duba lafiyan amininsa.
Da shigarsa kuwa mata sukafara shewa suna guda ga ango ga ango, babu Wanda ya kula ya hauwa sama burinsa kawai ya comma dakin maheer, ummice data fahimci kamar ba lafiya ba ganin yanayin hydar din yasa tabi bayanshi tana tambayar khaleel ko lafiya.
A gaggauce yai mata bayani cewar maheer din baiji masallacin fada ba kuma an kira wayarsa bai picking sannan min tambayi gateman yace baiga fitarsa ba.Idan hankalin ummi yayi dubu ya tashi itama tuni tabi layinsu.
  Murda doorknob din hydar yayi yaji a kulle kyam... Bubbugawa yashiga yi yana Kiran sunan maheer din amma shiru kakeji, ummima kiran sunansa tashiga yi amma ba amsa hakan yasa suka deciding su 6alle kofar.
Hakan kuwa a kayi sukayi amfani da wuka wajen balle hannun kofar tareda turawa da karfi.
A tare idanunsu ya sauka kan maheer dake zube a kasa sanye da farar shadda iri daya da hydar sai babban rigarsa da hula had'ida makullin motarsa yashe a gefensa, a lokacin basu lura da jinin daya 6ata masa gaban Riga ba saida hydar ya karisa da gudu ya juyo dashi.
  Ummi salati tasa tafara kuka nan danan, hydar kuwa jijjigasa yake hankali tashi.
"Maheer.... Buddy wake up, stop joking around."
"Ya khaleel this is not a joke can't you see blood ya staining masa Riga."
Sai a sannan sauran suka lura da jinin har a bakinsa da hannunsa.Hydar kasa ta6uka komai yayi sai jikinsa dake rawa.
Khaleel yayi azaman ta6a pulse dinsa yaji alamar akwai sauran rai a jikinsa.
"Let's take him to the hospital...."
Sai a sannan hydar din yasamu kwarin gwiwa....
"Ummi please control yourself... Addu"a yake bukata he'll be fine insha Allah."
Jinjina kai tayi tana kokarin daidaita nutsuwarta.
"Kubi ta back door dashi.... Mutane sun cika babban falo bansan Susan halinda ake ciki guri zai hautsine."
  Hakan kuwa akayi suka cicci6esa zuwa mota...sai ganin ummi da mayafi sukayi, khaleel yace
"Ummi dakinyi zamanki...Maheer will be fine,people wilbe suspicious idan aka nemi groom's mother aka rasa."
"Kaiya kyaleni ibraheemah... Meyafi ran dana, muje kawai."
Sai a sannan hydar yayi magana.
"Ba'ayi hakaba ummi dan Allah ki koma, zuwanki asibitin baida wani amfani a yanzu sai tashin hankali dazai Kara miki....kizauna kimasa addu'a insha Allah zai samu sauki, babu abunda zai sami maheer dinmu da yardar Allah."
Babu yadda ummi ta iya suka iya dole ta hakura, a hanya hydar yake sanar dasu Abba abunda ke faruwa sukace yanzu suna zuwa.
Acan kuwa baba yayi yayi adaura auren kafun abar gun abba ya kiya a cewarsa ba"a San meke damun yaroba kar a shiga hakkin yarinya.
  Babane yasanar da mai martaba abuda ke faruwa tareda bashi hakuri, yanuna masa ba komai lafiya na gaba da komai dan daganan saukar karatu zashi daya bisu asibitin.
  Daganan Baba da Abba da sauran yan uwa na kusa suka nufi asibitin.
  Da isarsu lokacin already an Shiga dashi emergency, Abba na zuwa ya kutsa kai ciki, sauran baba, sadeeq, hydar, khaleel, faruk sai muneer da ammar suka zauna waje hankalin kowa a tashi...kowanni addu'a yazo bakinsu yi suke.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now