In dedication to
Miemiebee 👄*****
Bud'e k'ofar tayi tana dubanta, juyawa zarah tayi tafara tafiya a dak'ile tace.
"Breakfast is ready."
Murmushi kurum miemie tayi dan abun dariya ya bata tana mamakin iron hali na mutanen gida,toilet ta fad'a tayi wanka bayan ta fito tayi sha'awar ta shirya cikin doguwar rigar atamfa saboda ganin yadda su zarah ke shigarsu ya bata sha'awa, bayan ta saka tafara kokuwar d'aura d'an kwali, kasawa tayi saboda bata saba ba, tsaki tarink'a ja k'arshe ajiyewa tayi ta yafa k'aramin gyale bayan ta combing kanta tayi packing.
Da sallama tashiga duka suka amsa mata,dukansu suna gun banda PMB had'a Ido tayi da jaleelah dake zaune gefen kujerar da murad ke zama taci uwar kwalliya cikin material lace fuskar nan tasha makeup wane gidan biki zata tayi mugun kyau,take taji wani Abu ya tokare mata mak'oshi, tarasa dalili duk sanda ta kalli jaleelah takejin abun nan musamman tagansu tareda murad.
Bayan ta gaida mai martaba yasanya mata albarka saboda sauk'in daya samu daga jiya zuwa yau.Murmushi d'auke a fuskarta tagaida hajjo ta amsa ba yabo ba fallasa bayan tamata wani kallon Dana kasa fahimta.
"Sannunku."taceda sauran tana murmushi, amatullah ne kurum tai mata d'an guntun murmushi, Sarah kuwa kallonta kurum tayi ta d'auke kai sai jaleelah data watsa mata mugun kallo.
"Jaleelah jeki dubo murad."hajjo tafad'a tanasawa mai martaba abinci.
Jiki na rawa ta mik'e sai karkada jiki takeyi miemie tabita da kallo ranta na mata wani irin zafi, ji yadda take tafiya tamkar bazata taka k'asaba sai rangwad'a take.
Gaba d'aya taji ranta babu dad'i, wani haushin jaleelah ne ya tokareta,ita Sam bata mataba, kaudi da kinibibinta yayi yawa.
Minti uku tsakani saigata ta dawo kamar data tashi Sama bakamar fitar ta ba, expression na fuskarta ta sauya daga fara'a zuwa tsumewa duka suka dubeta a kallo, miemie kuwa dariya ne ya taso mata dan dagani emperor ya gwada mata hali.
"Lafiya 'yar abba."mai martaba ya tambaya yana kallonta.
Tura bako gaba tayi takalli hajjo da ita ke mata mata kallon tambaya.
"Yace na fice shi aeki yake bazaici abincinba."tafad'a tana tura baki.
"Murad d'in ne yace haka? Baki cemishi ni na turokiba?"hajjo tafad'a rai a 6ace.
"Wallahi hajjo na fad'a mishi yace nazo nace miki bazai ci abincin ba, dana matsa ya tsawa ma ya dakamun saura k'iris ya filleni da mari."tafad'a tana goga hannu a ido alamar zata fara kuka.
A zuciye hajjo ta mik'e mai martaba ya dakatar da ita ta hanyar d'aga hannu yai mata alamar da ta zauna, babu musu ta koma ta zauna.
Ya dubi zarah da amatullah na d'an seconds k'arshe idanunsa ya sauk'a kan miemie dake cin abincinta.
"Mariam jeki ce yazo ina kiranshi."
"Na'am..."Babu shiri ta had'iye abincin dake bakinta har saida ta kusa k'warewa ta zaro idanu, duka suka kalleta, ganin kallon dasuke mata yasata saita kanta tareda murmushi ta d'aga kai, ahankali kamar wacce k'wai ua fashewa a ciki ta mik'e tayi d'akinsa.
A bakin k'ofa ta tsaya tana tunanin abun yi, gaba d'aya ta tsorita dashi a jiya ko wani mataki zai d'auka a kanta yanzu, Ita kanta batason abunda zaisa tazo kusa dashi saboda ta lura duk sanda suka had'u sai tayi abunda ba dadaiba, a yanzu tasan yamaida mahaukaciya bai ganinta daraja saboda dabi'unta kunyar had'uwa dashi take tasan shima bazaiso sake kallonta ba saboda abubuwan data mishi a zuwanta.
Daurewa tayi tafara knocking gaba d'aya jikinta a mace, takusa minti biyar tana bugawa babu alamar za'a bud'e, a hankali tasa hannu ta murd'a k'ofan cikeda tsoro takuwa ci sa'a a bud'e take, tun kafun tabud'e baki tayi sallama ta tsinkayi muryarshi.
"Don't you dare step a foot in this room leela,kafun ki k'ara 6atamun rai kiyi gaggawan tafiya dan kika kuskura kika shigo daga ni harke bazamu ji dad'i ba,sannan wannan ya zama gargad'in da zan miki kan shigowa d'akina bada izinina ba."yace cikin husky voice nasa.
D'aga kai tai ta kalle shi ta gefen d'akin,sanye yake da farin T-shirt sai dogon bak'in wando (sweatpants) gashin kansa a jik'e da alamar bai jima da fitowa daga wanna ba,yana zaune kan desktop computer da alamar aeki yake gaba d'aya hankalin sa naga abunda system d'in.
_bossy like always_ tafad'a a ranta abunda bata saniba a zahiri ta fad'a.
Jin muryar ya sashi juyowa ya kalli bakin k'ofa inda take tsaye tamkar statue, kallon daya mata saida gabanta ya fad'i,kallonsa kad'ai kashe mata jiki yakeyi.
Seconds suka d'eba suna kallon juna kowanne ya kasa magana a cikin su, kauda kai yayi yamayar kan monitor'n dake gabanshi.
"Mekike buk'ata..."ya tambaya fuska a d'aure batare da ya dubeta ba.
Had'iye yawu tayi tareda sauk'e ajiyar zuciya, bata taba tsammanin zai ragar mataba, amma ji bawan allah dukda laifin data masa a jiya baisa ya mata korar kare ko ya zageta ba, sai tambayarta ma da yayi me take buk'ata, saita k'ara jin haushin kanta ya lullu6eta bata San sanda tad'anyi murmushi tana kallon side view na fuskarshi, dogon hancinsa da eyelashes nasa sun fito sosae,beard dake fuskarsa ya k'ara masa kyau ta shagala da kallon sa.
"Me kike buk'ata?"ya sake maimaitawa,kunyar kanta taji yadda yakamata tana kallonsa.
"Dama..."
Bata idasa ba ringing na wayarsa takatseta, kallon fuskar wayar yayi tareda lumshe I do Wanda yake k'ara masa kyau, saida yayi d'an Jim kad'an sannan ya k'ara a kunne.
Dagacan aka fara magana idanunsa a lumshe amma yanayin fuskarsa yanuna rashin jin dad'in abunda wancan ke cewa.
"Khaleed I've never disappointed anyone before have I?...I worked very hard on that project,everything got ruined in the die minute despite spending weeks on it,I had to restart kuma kasan bazan yi aekin ha'inci saboda Sauri ba,we're talking about a factory it isn't easy ayi cikin kwanaki,but if you guys are in a haste I won't mind loosing the contract zaku iya sa wani yayi, I apologize again."yana kaiwa nan ya katse wayan tareda lumshe idanu ya ajiyewa phone d'in tareda da dafe kai.
Miemie dake tsaye jikinta yayi mugun sanyi, duk abunda yafaru saboda itane, da badan itaba da hakan bata faru ba,saboda ita ya loosing contract nashi Wanda ya bada time da lokacinshi wajen yi, haushin kanta duk ya gama rufeta bata san sanda tamatso kusa cikin nadama tace.
"Everything has happened because of me, I'm really sorry....really sorry."tafad'a kamar mai rad'a kanta a k'asa.
Bud'e idanu yayi ya kafa mata grey eyes nashi,itama shi take kallo idanunta hawaye ya cika suna shirin zubowa.
Ahankali takai hannu ta kama kunnuwanta.
"Sorry..."muryarta ya fara rawa hawayen ya gangaro.
"Sor...."bata k'arisa ba sakamakon mik'ewa da yayi cikin Sauri ya rik'o hannuwanta data kama kunnenta tareda sauk'ewa yana girgiza mata kai.
Kallonsa take idanunta cikeda hawaye shima yana kallon cikin idanunta, sakar mata hannu yayi cikin sauri tareda mik'a mata handkerchief dake gurin alamar ta goge hawayenta.
Kar6a tayi ta goge kamar yadda ya umurceta ta kalleshi.
"Am terr...
"Shhhh..."ya d'aura hannunsa kan bakinsa alamar tayi shiru.
"You shouldn't be sorry cause abunda ya faru allah ya Riga ya rubuta sai faru,I know you do believe in destiny tunda ke musulma ce besides I was supposed to apologize for being rude to you, bai kamata na fad'a miki haka ba I bursted my anger on you bacin kaddarar da allah ya d'auro mun kenan, I apologize."yafad'a bayan ya koma kan kujerar sa.
Da mamaki Miemie ke kallonsa, wannan wani irin mutum ne? Dukda abunda ya fad'a gaskiya ne but ya loosing babban contract Wanda she believed zaisamu millions akai, dan zanen factory isn't an easy task, amma alamunsa bai nuna ya damu ba saima bata hak'uri da yayi kan abunda ya fad'a akanta Wanda tafara yadda tanada ta6in hankalin.
"And about the contract?"tafad'a tana kallonshi da mamaki.
"I don't mind loosing it,I doesn't work cause of money, kud'i ba matsala bane a gidannan ina aekine saboda sha'awa da kuma neman na kaina da kuma al'umma, so it doesn't matter don nayi loosing, k'ila akwai wani dalilin da allah yasa na rasa, allah sa hakan shi yafi alkhairi."
Kallonsa kawai miemie keyi speechless,bazata bari ya loosing ba she definitely has to do something, she'll make up everything she has done.
"Thank you."tafad'a a hankali tana murmushi.
Hankalinsa naga monitor yace.
"Ehm... Meya kawoki?"ya fad'a fuskar kamar ko yaushe.
"Abba ne yace na k'iraka."
Mik'ewa yayi tareda nufan closet yace.
"I'll be there in a jiffy."ya shige ciki.
Miemie dake tsaye ta bishi da kallo, komai nasa abun burgewa ne, girgiza kai tayi tareda ficewa rik'e da handkerchief daya bata.
Da shigarta dining room d'in kowa ya kallota dan ganin yanayinta, fara'ar da take ya mugun bash mamaki dan da wuya ku had'u da PMB ku rabu rai bai 6aciba, itakuwa fuska a sake ta zauna tareda duban mai martaba tace.
"Yana zuwa yanzu."
Jaleelah dake watsa mata wani kallo taja d'an guntun tsaki Wanda ya jawo hankalin kowa kanta, mai martaba yayi murmushi Wanda shi kad'ai yasan manufarshi.
Miemie ta d'auki juice tamik'awa jaleelah tana murmushi.
"Here you go...you must be thirsty saboda baba yace duk mai jan unnecessary tsaki acikin uku za'a samu d'aya,in ma ransa a 6ace inma ya had'a dangi da tsaka kokuma harshensa na rawar shoki..."
"Hahahaha...."amatullah ta kwashe da dariya, Sarah kuwa hak'oranta ne suka fito waje.
Da mamaki hajjo da jaleelah suka kallosu, da sauri suka maida dariyar.
"Yaran Abba fara'a nada kyau kuma yana haskamun ku, kuci gaba da fara'a don allah."mai martaba yafad'a yana murmushi.
Jaleelah ta k'ulu iya k'uluwa amma ta kasa tashi tabar gun illa tura baki datayi tahad'e gira.
Hajjo kuwa ita kadai tasan abunda ke ranta ta maida kanta kan abincinta.
Ko minti uku ba'ayi ba saiga PMB ya shigo cikin wata shiga daban yaja kujerar gefen jaleelah ya zauna opposite da miemie.
Bayan yai ma mai martaba sannu yajuya kan hajjo wanda kamar zatai masa magana ta fasa.
Bayan sun gama breakfast data koma d'aki ta d'auko makeup kit bata Wanda bayan power babu abunda tasan amfaninsa, so take ta gwada kwalliya tayi kyau irin na jaleelah tarasa dalilin tin hakan amma a bata ko kozata daina mata kallon rainin wayo, a tunaninta batada kyaun jaleelah.
Kasa komai tayi a gun a hankali ta mayar, data biye addah abeedah da tuni ta koya.
Tsaki tayi ita bataga dalilin sauya kanta ba saboda jaleelah, she'll always be her real self.
Harta mayar takasa daina tunani ta d'auko ta dinga mulke mulkenta ta goge bayan ta gala dariyar kanta don dodo ta dawo, k'arshe wanke fuskarta kurum tayi tafice ta zuwa yiwa mai martaba exercise.******
A ranar aka mata delivering laptop d'in, bayan ta gama aekinta hartamaida mai martaba d'akinsa ta Shiga d'aki tareda transferring komai daga old Macbook d'in zuwa sabon da taimakon yah faruk da allah.
Wanka ta shiga tareda wanke handkerchief da PMB ya bata d'azu don maida masa da kayansa.
Bayan sun having dinner Wanda kallo kurum ke shiga tsakanin su.
Tsaye take a k'ofar d'akin sa rik'e da sabo da tsohon laptop d'in bayan ManSadi ya shaida mata yana ciki, kasa knocking tayi tana tsaye gaba d'aya jikinta ba lakka.
PMB dake tsaye yana Zane hannunsa rik'e da cup na coffee yana sipping.
Knocking yaji a k'ofarsa mamaki ya kamasa sanin ManSadi kurum ke iya zuwar masa d'aki a wannan lokacin.
Ta spyhole ya duba yaga miemie tsaye sai rarraba idanu take,tambayar kansa yayi me ya kawota d'akinsa wannan lokacin.
Ji tayi an bud'e k'ofa, a hankali ta cusa kai tareda sallama, saida ya isa inda ya bark Kafin ya amsa.
Kallon juna sukayi tai masa murmushi yayi saurin kauda kai ya ajiye mug d'in hannunsa tareda nad'a hannunsa a k'irji ya lumshe idanu kana ya dubeta.
Miemie ta matso kusa da shi tana murmushi.
Da mamaki Yake kallonta zaiyi magana tayi saurin cewa.
"I promise to fix everything remember?"ta d'aga masa gira d'aya tana murmushi.
"You won't loose the contract insha allahu saboda komai ya dawo dai dai, you can proceed from where you stopped."
Still yana tsaye da mamaki.
Fito dasu tayi daga bayanta ta mik'a masa.
"Here you go...I transferred everything daga scrap one d'in zuwa sabo."tafad'a tana fad'ad'a murmushinta.
Maimakon taga yayi farinciki saima had'e fuska daya kuma yayi, canza fuska tayi tana kallonsa.
"Meyasa kake tsumewa? Ain't you happy?"
"I don't remember asking you to repay me, bance ki biyani ba dan haka ki tattara kibar nan."ya fad'a rai a 6ace yana nuna mata hanya.
"But..."
"Get out..."ya d'aga murya.
Bai bari tayi magana ba yaje k'ofa tare da bud'ewa yai mata alamar ta fita, jiki a sanyaye tana waigensa ta fice hawaye na zubo mata na takaicin abunda ya mata.
Rai a 6ace ta shiga d'akin tareda banging door d'in, zuba laptops d'in tayi akan gado tareda nad'e k'afafu ta zauna kan gadon, wannan ma ae iskanci ne, ya'za'ai ta taimaka but he open a can of worms for her, itafa ba biyansa tayiba.
Share hawayenta tayi tanata masifarta ita kad'ai, dayasan stress d'in data shiga akai dabai mata hakaba.
Tanadaga zaune taji Abu na murk'ususu k'asan pillows na bayanta, tsoro da fargaba suka shigeta,da sauri ta sauk'a akan gadon tareda janye pillows din.Wani razanannen ihu tasa Wanda ya amsa duka mansion d'in.*****
Comment, vote. And share
OneLove ❤❤❤
ŞİMDİ OKUDUĞUN
SAUYIN RAYUWA (EDITING)
Romantizm"What the__ what the__ what the__ He always shouts unnecessarily emperor is too much."She hissed irritatedly. "Princess if anyone tries to harm you do not hesitate to tell me...it isn't late to back out of this contract"He Sounded very worried "No...