chapter 53

1.7K 152 16
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

*******
"Subhanallah... What the..."yayi saurin duk'awa inda mug din ya bugi k'afarta.
Da mamaki ya d'aga ya dubeta gaba d'aya she's restless ko gizau batayi alamar bata ma San taji ciwo ba.
Mik'ewa yayi yana kallon fuskarta curiously.
"What's going on doctor?"yana kallon fuskarta.
Sai a sannan tad'ago ta dubeshi idanunta sunyi narai narai.
"Hope baka shaba?"
Lumshe idanu yayi tareda shafa kansa cikeda takaici.
"Ya za'ai nasha bacin kin zubar..."
Ajiyar zuciya ta sauk'e zata sake magana yayi saurin katseta.
"Shut up... You're hurt."batare da ya saurari abunda zatace ba yayi saurin janyo hannunta ya zaunar kan kujera.
Sai a sannan tafarajin zogin da k'afarta keyi tafara runtsa Ido tana cije le6e alamar zogi.
Sosae ganin ta haka yasashi zama worried and uneasy, yadubi sadi daya biyo bayan miemie.
"What the heck are you still doing here..."da sauri ya juya dan ya gane abunda yake nufi.
Hura mata k'afar yafara tamkar hakan ne zaisa tadaina jin zogin.
"What the hell were you thinking ms. Clumsy,see what you've got yourself into,you don't know how worried I'm seeing you like this"yafad'a tamkar zai mangareta.
Haushine ya turnuk'eta ganin yana mata masifa ga kuma zogin da k'afarta keyi, tayi saurin Jan k'afar a hannunsa cikeda masifa tace.
"Let go off my ankle bana buk'atar taimakonka in haka zaka tayimun masifa,da wanne zanji da zogin da kafata keyi koda masifar dakakemun huh? na isa na canza abunda allah ya tsarane...I don't need your help I can take care of myself"tanakaiwa nan ta murguda masa baki tareda mik'ewa,taku daya taxi da sauri ta koma ta zauna jin azabar da k'afar keyi.
Duk abunda take yana tsugune agun yana kallonta.
D'aga ankle din yayi tayi saurin kwacewa cikeda masifa shikuwa yasake damk'owa yadubeta cikin fad'a yace.
"Idan kika sake ja saina mangareki..."
Nitsuwa tayi ganin babu wasa tattare dashi shikuwa dan murmushi yayi ganin yadda tayi.
Daidai lokacin sadisu yadawo rik'eda ice block da first aid kit a hannunsa.
K'arban Ice d'in yayi miemie ta zaro idanu tareda duban k'afarta inda yayi jaa.
"A ina za'asa wannan?"
"A bakina..."yabata amsa bayan ya tamke fuska.
Jin amsar daya bata yasa taxi shiru tareda tura baki.
K'ok'arin mannawa yake ta rik'e wrist nashi tana girgiza kai pitifully...d'agowa yayi yadubeta ganin yadda ta marairaice masa tamkar zatayi kuka.
Saukar da idonsa yayi da sauri ya had'a hannunta biyu ya rik'e da hannu d'aya, d'ayan kuma yayi amfani dashi wajen sa ice block din akan k'afar, yana kallon yadda take tuntse runtse saboda zogi a hankali zafin yafara lafawa har ta dawo daidai.
Yana cirewa sadisu ya mik'o masa ointment, bayan ya shafa ya rufe gurin da bandage, duk abunda yake baiko kallonta itakuwa idanunta a kansa tanajin wani Abu na yawo a jikinta tanajin wani strange feelings.
Bayan ya gama ya mik'e daga tsugunon dayake ya dubita tareda zuwa hannu a cikin aljihu yana kallonta a hankali da sauk'ar da idanunta kamar mai tsoron wani
abu.
"Are you okay?"ya tambaya yana kallon fuskarta.
D'aga masa kai kurum tayi zata mik'e yayi saurin mata alama da hannu takoma ta zauna.
"Tell me..."
"What?"ta tambaya.
"Meyasa kika zubar mun da coffee?"ya tambaya bayan ya tamke fuska.
"Ah... Am..."ta d'aga kai ta kalli sadisu inda shima kallonta yake yanason sanin dalili.
"Nothing..."tabada amsa bayan ta kauda kai.
"Look at me..."ya fad'a in a bossily manner
Kasa hada Ido tayi dashi tana kallon kasa.
Saida ya maimaita tadago tadubi shi cikin idanunsa masu bata tsoro.
"Do I look like a kid to you?"
Ta girgiza kai kamar wata sokuwa.
"Then I ask for the last time meyasa kikayi haka?"
"For fun..."
Dan murmushi kadan yayi.
"And you think I'd believe this ko? Don't tryna fool me doctor nasan you did it on purpose..."yafada yana kallonta suspiciously
Narai narai tayi da Ido kana tace.
"Your coffee has been poisoned..."
Da mamaki duka suke kallonta, tad'ago Ido tana kallonsa.
"Your coffee has been made with hemidactylus frenatus kuma they make use of the poisonous one..."tafad'a with full of emotions in her eyes.
"They're after your life emperor..."finally hawaye ya cika mata idanu cikeda tausayinsa.
He stood there speechless yana kallonta cikin yanayi mai wuyar fassaruwa.
"Ya akayi kikasan da hakan?"yayi k'ok'arin furtawa still idanunsa akanta.
To anzo gurun, kallon sadisu taxi inda shima yakeson jin bayanin yaakayi tasani bacin komai tare sukeyi.
"Ever since da nafara ganin scary messages da maciji a dakina sannan da korata da kayi da farko I know something is definitely fishy somewhere,daga lokacin nafara bincika duk wasu Abu dake cikin gidan nan saboda from my view babu Wanda zaimun haka sai Wanda ya sanni I mean Wanda yayi hakan a cikin gidan nan yake, the first person that came into my mind was mermu, da farko naso kawar da tunanin but lokacin dana ganta a dakina ya tabbatar mun da bata da gaskiya, kuma akwai wani k'ofa da ta ta6a nuna mun kan cewa babu Wanda yasan da gurin bayan ga ku sai itada sadi I believe tagun aka shigo akasamun maciji,so I followed her to her room that night na wurga recorder cikin dakinta batare da tasani ba, sannan na connecting da MacBook dina saboda inajin duk wani conversations nata almost 4days yanzu, tunda nasa banji wani Abu ba sai dazu immediately when I woke up Inda take magana da wani kan cewa ta aiwatar da abunda aka sata, she make your coffee with a poisonous lizard kuma har ankai maka nan da 30mnts zaka mutu so I quickly called ManSadi to stop him from bringing it you unfortunately yaci yakai already so I ran towards here luckily I came on time otherwise..."ta girgiza kai hawaye ya zubo mata.
Tunda tafara magana idanunsa akanta ko kyaftawa bayayi gaba daya jikinsa yayi la'asar yana kallonta cikin wani yanayi ahankali bakinsa ya iya furta.
"You saved my life?"
"Not for the first time yalla6ai, but for the second time."cewar sadisu
"Doctor has been there for you through everything, she manage to prevent you from going out yesterday by distroying your project baka saniba cause an kunce maka tayun mota..."
"What?"
"Akwai inda mukejin conversation din wasu mutane biyu a cikin gidan nan Wanda ciki harda brothern mermu inda aka basu umarnin yin hakan amma har yanzu bamu gano wake sasu hakanba."
Nan yabasa labarin inda akayi suka fara gano haka sannan ya k'ara da cewa.
"Doctor tace kar a sanar dakai saboda yin hakan zaisa su iya sauya plan cause zasu gane dan suna following kowani moves naka,sai mun gano asalin shugaban kafun mu sanar dakai."
Duk abunda sadisu ke fad'a idanunta murad maga miemie yana mata wani kallon da ni kaina nakasa ganewa.
"Why didn't you tell me?"
"Cause I know bazaka ta6a barina na taimaka ba cause kadaukeni as a fool bansan abunda ya daceba."
Ahankali ya k'arisa gabanta ya tsuguna kamar d'azu yana kallonta, kallonsa itama take hawaye fal a idonta.
"Am sorry..."ya furta da wani irin murya daya kashe mata jiki
"And Thanks for everything..."
Girgiza kai tayi a hankali bakinta ya kasa furta komai.
"If it wasn't for you I wouldn't be alive by now..."yafad'a emotionally
"Your shouldn't thank me emperor, all thanks to Almighty daya kaddaro hakan, mu fawwala masa komai insha allah he'll see us through this, and you've to be extremely careful cause your enemies are surrounded by you..."tana kaiwa nan ta mik'e ahankali tafara d'ingisa kafar saura kad'an tafad'i yayi saurin tarota.
Kafun tayi auni ya d'agata in a bridal style, batayi k'ok'arin hanshi ba cause tasan ba iya tafiya zatayi ba, kallonsa take yasauk'ar da ita har zuwa d'akinta ya ajiye kan gado tareda jawo conforter ya rufeta.
Tsugunawa yayi saitin fuskarta
"Have some rest...you shouldn't stress yourself and incase if you need something don't hesitate to call zarah okay?"
Ahankali ta girgiza kai ya mik'e ya fice, tsintar kanta tayi dabin bayansa ta murmushi tanajin kanta cikin wani yanayi ahankali ta lumshe idanunta amma tayi saurin bud'ewa sakamakon ganin fuskar emperor na mata gizo.
"What's wrong with me?"ta tambayi kanta
"Why am feeling strange whenever am with him?"babu amsa
Haka tayita tambaye tambaye tana sake sake kamar mahaukaciya har bacci ya sureta cikeda mafarkan emperor.

_*BAUCHI...*_

komai ya kankama gameda shirye shiryen auren maheer da miemie, babu Wanda baiyi farin ciki da faruwan hakaba musamman hajja ganin maironta ta kusa auren Wanda yafi kowa kaunarta a duniya, ba ita kadaiba hatta ga mama tayi farin ciki matuk'a saboda tasan maheer mai iya rik'e miemie ne a kowani hali, kaunar junansu daga allah ne babu Wanda zai iya rabasu,daga kan sadeeq zuwa kasa duk sunyi matukar farin ciki da faruwar hakan saboda babu abunda yafi musu ganin miemie ta aure maheer, wani uban gayya dayake ganin yafi kowa sa'a a duniya ganin zai mallaki muradin ranshi dan itace rayuwarsa, kaunarta a jininsa yake kuma yanajin babu mai iya rabasu sai Allah, har a lokacin babu Wanda ya sanar da ita wani Abu saboda sunaso subata pleasant surprise dan sunsan zatafi kowa farin ciki da hakan, shi kansa maheer ya kasa sanar da ita komai saita dawo zataji dan a yanzu yariga da yasan miemie na Sonsa kamar yadda yake sonta dan wani sa'in hirarsa is more like na masoya hakan yasa baida damuwar komai, babu abunda yafi burgesa irin yadda ya lura rayuwar miemi ya sauya bakamar yadda take da ba,muryarta ta sauya dan a hankali take magana kuma duk abunda zai fito daga bakinsa sensible ne, komai nata a nitse takeyi hakan yasa yake tunanin ko son da take masa ne ya haka,komai na tafiya masa yadda ya kamata kuma a kullum Kara kaunar miemie yakeyi.
Duk wasu formalities na neman aure anbi ansa aure nan da 6weeks immediately dawowan miemie, mama da ummi na shirin zuwa Dubai wajen had'owa miemie kayan d'aki da lefe, komai na tafiya yadda ya kamata.
A yau Monday maheer wuni yayi a gida baisamu damar zuwa asibiti saboda zazza6in sa daya dawo sabo, da ummi ta gwada temperature nasa saida ta tsorita,babu yadda batayi dashiba suje asibiti abba ya dubasa yaki acewarsa zai ware kamar ko yaushe Hutu kawai yake buk'ata sannan yaki a sanar dakowa musamman miemie, Sam ya kasa cin komai ganin haka ummi ta d'aura masa ruwa ko zai danji k'arfin jinkinsa,haka suka wuni ana abu d'aya.
Da yamma lis ummi tana kitchen itada safara suka tsinkayi sallama daga falo.
Wanke hannunta tayi ta cire apron din jikinta tafice.
"Aah jameela sannu da zuwa."
Murmushi meela tayi tana tsaye a kunyace rik'e da leather a hannunta.
"K'ariso mana ya kin tsaya kamar wata bak'uwa."ummi ta wangale mata hannu.
A kunyace tak'arisa ta shige,har kasa ta tsuguna ta gaishe da ummi ta amsa cikeda fara'a.
"Jameela kinyi wuyar gani, koda yake bana ganinki sai mummynki ta aeko ki."ummi tafad'a tana mata hararan wasa.
Murmushi tayi a kunyace tace.
"Ba haka bane ummi yanayin aekinmu ne babu lokaci shiyasa."
"Na karbi uzurinki."
Bayan proper gaisuwa ummi ta k'ira safara ta kawo wa meela drinks sannan tamik'a wa ummi leather'n dake hannunta.
"Gashi mummy tace ga gudunmawa na kawo miki kiyi hak'uri na yawa."
"Ahhh ji asma'u da wani zance, harda dawainiya haka kice mata na gode sosae dan mata yana godiya..."
Sadda kanta tayi kasa, meye kuma na maheer a ciki bayan kayan matane a ciki, ganin yanayin data shiga ummi tace.
"Jameelah kaddai kicemun bakisan yayan naki ya kusa aureba?"
Dammm taji gabanta ya buga,da sauri ta d'ago kai ta dubi ummi dake murmushi,gaba daya jikinta yahau rawa k'ok'arin daidaita nutsuwarta tayi ta k'ak'alo murmushi.
"Allah sarki banda labari allah ya sanya alkhairi wacece matar?"ta tambaya batare da ta saniba.
"Miemie..."ta dakata jin wayarta na ringing,excusing kanta tayi kana ta amsa.

*******
TeamMurad
TeamMaheer

Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now