chapter 63

1.5K 156 57
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

******
  Sake goge idanunsa yayi Karo na biyu dan tabbatar da abunda idanunsa suke gani ya sake bud'e yaga wayam tabbacin bata gurin
"Where could she have gone?"ya tambayi kansa a hankali kwakwalwarsa ta kasa zama saiti.
Cikin tashin hankali yafara.
"Duckie joke apart wannan ba lokacin wasa bane, don't even start this,you really need to come out hide and seek din ya isa haka..."yafad'a a cikin tashin hankalinsa da tunda yake a rayuwarsa bai ta6a shiga ba.
Sauri sauri gudu gudu ya k'afisa gindir bishiyan abunda ya gani ya mugun dugurguza masa hankali.
Wayarta da mayafin data rufe kanta tun tasowansu ne yashe a k'asa, daskarewa yayi agurin yakasa ta6uka komai, gaba d'aya jikinsa rawa yakeyi...kansa na mugun sarawa da sauri ya dafe.
Kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya tsugunnan ya d'auka a hannunsa yana kallo, lokaci d'aya idanunsa sukafara dishi dishi hawaye na neman cikasu.
Girgiza kai yayi kamar zararre yafara cewa.
"This can't be...please don't do this to me Duckie..."da sauri yahad'iye abun da ya tsayamar a wuya.
  Duk yadda akayi d'aukar ta akayi, amma abun tambaya anan shine,idan ubalili ne shi sukeson kashewa ba duckie ba,how comes sun d'auketa silently batareda sun attacking nashi ba,girgiza kai yayi yace.
"I know you're just kidding..."
Wannan baiyi kama da wasa ko kad'an, a state din daya barta bazata iya koda tafiyan minti uku ba bata fad'i ba,kuma duckie'n sa daya sani she's very brave bazata ta6a bari a dauketa batareda wani sign ba, saidai an taking advantage na halin datake ciki.
Kallon jejin yayi inda ko alamar rai babu aciki,sai kukan tsuntsaye da tafiyan ruwan,a iya saninsa babu namun daji a gurin balle ace sun tafi da ita kuma koda akwai zaiga jini, duk yadda akayi wasu daban ne suka d'auketa,He can't let anything bad happen to her, he can surrender idan yin hakan shi zaisa a sake ta ita he hope ba wasu mutanen banza bane suka dauketa, duk ya kasa tsayar da kwakwalwarsa tamasa tunani mai kyau dan gaba d'aya a rud'e yake.
Ganin fa tsayuwar dayake a banza ne yasa yayar da bottle din hannunsa yashiga kwad'a mata k'ira yana nemanta duk k'arfin da allah ya bashi yanaji kamar zata amsa mishi amma a banza.
  Lokaci d'aya ya fita hayyacinsa ganinfa da gaske miemie bazata amsa ba, idan kaganshi saiya baka tsoro had'i da tausayi kamar ba Prince Murad Bayero ba,mutumin da bai damu da kansa bama balle wani, mutumin da Sam harkar wani bata dameshi ba balle ya shigeta, mutumin ba kallon mutane bai ishesa ba balle har ya damu dan sun tafi, mutumin da Sam amutu ko arayu bai damesa ba amma yau akan miemie ya haukaci lokaci d'aya dan bai ganta ba _so sad._
  Shiga kurum yake baisan inda yake zuwa ba, gaba d'aya voice nasa kakeji yama kwadawa miemie k'ira hannunsa rik'eda mayafinta da wayanta, shikansa baisan yana hawaye ba jikinsa ko ina rawa yake har bakinsa yakasa magana sai la66ansa dake motsi.
Tsayuwa yayi cak komai na jikinsa ya tsaya sakamakon ganin rigar jikin miemie a k'asa (rigar Fulani data sa) tsugunawa yayi a gurin tareda d'agowa, da sauri ya sake a k'asa sakamakon jini daya gani a jiki ya shiga waige waige hawaye na sunturi kan fuskarsa duk yadda akayi she's somewhere near and in danger.
  Hayak'in daya hango asama na tashi yasa k'irjinsa ya buga dummm...
Mik'ewa yayi tareda rugawa a guje yanufi inda ya hango tashuwar hayak'in.
  A hankali yafara bin tacikin duhuwan ganyayyaki batareda da tsoro ko fargaban wani abu ya sameshi ba, burinsa kawai ya cimma gun yana fatar miemie na gurin, dab ya Ido inda yakejin shesshekan dariyar gardawa gawarin sigari da wiwi kota ina,a sannu yafara jiyo magana ganun inda wani gardi ya bud'e murya yace.
"Nalura har yanzu yarinyar nan da sauranta...yakamata mu dau mataki..."
"Oga ka kwantar da hankalinka, tunda tana hannunmu a sannu zata sanar damu komai, ko kuma shi ya fito nemanta... Kardai ka sanar da ubalili wani abu tukunna harsai komai ya wakana..."cewar wani cikin muryar maye.
"Kai dallah virus rufa mana tsamin bakinka dan kutumar ubaa,ka wani zak'e kana zubawa mutane shirme,zancen kud'i ake anan kuma shi muka fito nema bazamu bari damar nan ta wucemu ba, ko bakasan cewa awanni biyar aka bamu."cewar wani cikin d'aga murya.
"Dad'ina dakai wawane aradu,dani dakai bansan wake cikin mayeba, hanzarin me kuma zakayi bayan yarinya tak'i magana, kaduba babu azaba da bamu bata ba harda gusar mata da hankali kozata fad'a cikin maye amma takiya,mekuma ya saura da za'ayi banda abi a sannu aga ko shi zai fito nemanta."
"Ji mana baaba kadaina mana zancen banza anan,kakuwa San ubalili yamana alk'awari idan muka nemo su,kai yaushene ma kafara aeki damu dahar zaka nuna mana abunda ya dace dan kutumar ubaa kawai..."
"Kardai kasake zagin ubana dan aradun allah saina fitar maka da jini..."ya zaro adda
Nanfa fad'a ya kaure harsaida ogan ya tsawatar musu.
Bayan ya rurruga musu ashar Abu ya lafa dayan yace
  "oga manta dashi bai cikin hankalinsa, kabani dama nasa yarinyar nan tabud'e baki tayi magana..."
"An baka... Kasa tayi magana yanzu yanzu musamu mu aewatar da aekinmu mubar nan tun kafun lokaci yak'uri "cewar ogan cikin kakkaurar muryar.
Har a lokacin murad ba k'arisoba but yanajin conversations nasu.
"Ke ki sanar damu inda yake tun kafun namiki illa..."yaji k'arar mari
Wani mahaukacin dariya ta kwashe dashi Wanda dagaji kasan tana cikin maye.
"Wa... Shi... Shi kukeson na nuna muku inda yake, yana can cikin giwa a jejen Zimbabwe..."ta kumasa dariya.
Alamar zaro wuka yayi cikin d'aga murya yajawo gashin kanta daya rufe mata fuska ya saita wukar daidai wuyanta yace
  Da sauri yasa hannu ya baza ganyayyakin daya masa katanga da gurin.
Miemie ya hango an daddaureta jikin bishiya da igiyoyi, rigarta fari long sleeve gaba d'aya jini ya 6ata,goshinta kuwa jini na zuba.
Ganin an saita wuk'a daidai mak'ogoronta da yadda wancan d'in ya Cafko gashin kanta itakuwa ta runtsa ido tana dariya.
  Shikaran kansa baisan ya akayi ya isa gurin ba sai cafko mutumin tayi tareda basa wani naushi saida yayi baya a gigice.
  Kafun yayi wani yunkuri biyu daga ciki sun cafko hannunsa ta baya tareda rik'esa gam sai wulla k'afa yake yana k'ok'arin kacewe ya kasa rik'on da suka masa bana wasaba,shiko gaba daya hankalinsa naga miemie burinsa kawai ya isa gareta ya bata taimako.
Miemie kuwa idanunta sai lumshewa suke gaba d'aya tana cikin maye (intoxicated)Bakinta na son furta magana amma takasa idanunta sunyi jaja zir.
Bayi auniba yaji akima masa naushi a gefen fuska, abunku da farar fata saida gefen bakinsa ya fashe.
bud'e idanu yayi sai ganin wani basamuden mutum a gabansa fuskarnan baki k'irin idanunsa kamar gauta rik'eda cigarette a hannunsa yana zuk'a.
Murad ko k'ok'arin kwacewa yake amma ina sarkin yawa yafi sarkin k'arfi.
"What the hell have you done to her you son of a bitch..."ya fad'a yana cije hak'ora kafun ya k'arisa ya kuma kai masa naushi d'ayan gefen.
"Just let her go if not you'll be the one to suffer..."yakuma fad'a batareda ya daddara ba.
"Waye kai dazaka bani umurni har na nabi..."
"It's none of your business... Take me if you want but just let her go she has no business with you... Ni kukeso ku daukeni ku kyaleta."
Dan dariya mutumin yayi yace.
"Kayi tunani Mai kyau gaskiya,ban sankaba kuma bandamu na sanka ba, aekin kudi nake dole na kaika kamar yadda aka buk'ata... Ba laifi idan mun tafi da ita dan kai inaga lahira zakaje..."
"What the..."yayi k'ok'arin kwacewa rai a mugun 6ace.
"Don't you even try this... Am warning don't you dare touch her..."
"Wow! I so much love your courage...by the way ba wannan bane a gabana, zamu kaika inda ake buk'atar ka saboda abiyamu muyi gaba, itakuwa na rana d'aya muke buk'atarta daga zarar mun gama da ita saimu yadda ta ko ya kuka gani guys..."a tare suka kwashe da dariya.
Murad duk iya k'ok'arinsa wajen ganin ya kwace amma ya kasa, ga miemie can tana halin ha ula'i gaba d'aya zuciyarsa tafasa take had'i da tausayin miemie shi bai damu da abunda zai samesa ba ita kawai yake tunani.
Yana ganin sanda mutumin ya zaro waya a aljihu alamar zaiyi waya dasauri murad yace.
"Please ba dan niba dan allah ku kyaleta ta tafi..."yafad'a pleadingly sounding heart broken
"At last ka ajiye ego naka a gefe kana pleading kai ba sarki bare malam ballantana mu saurareka, am sorry to say babu ja da baya akan abunda mukayi niya..."
"Money... Are you doing all this for money?"ya tambaya disappointedly
"Yes you're damn right... Kudi kudi kawai mukeso indai a kwai kudi tofa komai zamu iya aekatawa dan musamesu koda kuwa kisan kai ne..."
  Murad ya girgiza kai cika da takaici yace.
"I can give you any amount muddin zaku kyaleta ta tafi..."
Dariya suka kwashe dashi duka suna k'are masa kallo cikin kayan jikinsa dayadda rana nayau kurum ya kodar dashi gashi har a lokacin bai cire beard dinba yananan kamar dan kauye.
  "Really?"suka sake tuntsurewa da dariya.
Murad yace
"Kufad'i duk nawa kikeso I can double the amount akan Wanda ubalili suka muku alk'awari..."
"250,000thousand... Kai ina kaga dubu d'aya ma balle har ka ninka..."
Jifa akan dubu daribiyu da hamsin suke k'ok'arin kashe rai, allah ya shirya mana duniya yasa mufi k'arfin zuciyoyinmu yasa mu daina aekata sa6o saboda abun duniya.
  Murad yace.
"Akwai agogo a hannuna you can take that it's worth morethan 500,000thousand."
  "What?"suka kwalalo idanu a tare.
Hannunsa inda suka rik'e ogan ya duba tareda zaro idanu, da sauri ya d d'ago ya dubi murad ganin dagaske yake agogon nada masifar tsada kuma wane da wane ne suke sawa.
"Let go of him..."cewar ogan
A hankali murad ya ciro agogon ya mik'a masa kana yace.
"Here you go, release her..."
"We'll but munaso musan wanene kai da ubalili suke nemanka..."
"Wannan ba damuwarku bane...ku saketa ku tafi, idan wannan bai isa ba ga wani..."
Ya fad'a tareda ciro duk wasu kud'i dasuke aljihunsa Wanda akalla zai kai 150,000thousand had'e da ciro iPhone7 dinsa ya mik'a wa ogan...
Kasa amsa yayi yasake baki yana kallon murad, duk yadda akayi wannan ba k'aramin mutum bane, kuma da gane he's innocent, then why are they after his life koma dai yaya su kudi sukeso sauran bai shafesu ba.
Sa hannu yayi ya amsa kana yadubi dayan yace.
"Virus kunceta..."
Lumshe idanu murad yayi alamun nasara.
Da sauri ya k'arisa inda take gaba d'aya galabaita had'e da maye sunci galaba akanta.
Kuncota dayayi zata fad'i da sauri murad ya tareda,sa hannu tayi ta kank'ameshi tsam kamar wacce za'a gudu da ita take neman taimako.
Shima rungumeta yayi tightly tareda lumshe Ido yanajin wani abu na ratsa jijiyoyin jikinsa wani 6angare na zuciyarsa na fararin ceton rayuwarta dayayi tareda bakin cikin ganinta cikin maye wannan yasan shine sila, yayi Dana sanin barinta ita kad'ai.
Ahankali yafurta
"Am sorry Duckie..."daidai kunnenta itakuwa Sam hankalinta bai jikinta.

*****
  Vote, comment. And share

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now