chapter 38

1.7K 138 15
                                    

In dedication to
Miemiebee 👄

*****
"Murad mekakeyi haka?"hajjo ta d'aga murya tareda matsowa kusa dashi.
"Banjin abunda ya dace fito daga bakinki kenan saboda kina ganin abunda ke gudana a yanzu, so please karki hanani aewatar da abunda nayi niya."yabata amsa batareda ya dubeta idanunsa naga Miemie sannan bai sauk'e bindigar ba daya manna mata a ka ba jikinta sai mazari yakeyi tana matse k'afafunta saboda fitsatin daya matsota.
"Don't you dare use that tone with me young man,dont forget that am your mother..."ta tsawatar masa.
Bai kulata ba yadubi miemie da gashin kanta ya gama rufe mata fuska sai idanu kurum ake gani.
"Ina jinki...you better speak up or I'd shot you."yafad'a cikin 6acin rai.
"Murad da hankalinka kuwa...
"Ina sane da abunda nake,sanin kankine bana son ana tursasani kan abunda banyi niyaba,so please stay out of this i'll handle her myself."yafad'a ransa a 6ace bayan ya runtsa idanu.
  Miemie kam tagama tsorita shikenan mutuwarta tazo bakinta sai rawa yake ta kasa magana.
"Murad likitan mai martaba ce ka sauk'e nace."hajjo takuma fad'i.
  Bai amsata ba sannan baida niyar sauk'e bindigar, ta kuma maimaitawa.
"Umma please...kema kin fad'a likitan mai martaba ce meye gamina da ita da har wani Abu zai kawota d'akina kuma a wannan lokacin? ba abun yarda bace..."
"She's innocent murad ya za'ayi tayi magana bacin wannan abun daka manna mata akai,yama za'ai tayi ihu inhar dawani niya tashigo"
Kallon hajjo yayi da mamaki.
"Ahh! I don't know what to believe umma,she was caught red handed shiyasa tafara creating scene anan,so is better if you don't drag yourself in."yafad'a irritatedly.
"Murad zuciya karta d'ebeka ka aekata abunda bai daceba,drop down the gun and listen to me, she's innocent."
  Girgiza kai yayi a hankali yace.
"She doesn't seem like one,she's either a stalker or a whore."
Cikeda tsoro miemie ke girgiza kai she's either a stalker or a whore shine kalmar daya tsaya mata a mak'oshi,tunda take a rayuwarta babu Wanda yata6a jifanta da wannan kalmomin,girgiza kai tafara bata San sadda hawaye ya cicciko mata ba Karon farko a rayuwarta da wani yata6a sata hawaye.
"Murad nace ka sauk'e Idan na isa dakai."hajjo tafad'a cikin d'aga murya.
Jikinsa ne yayi sanyi a hankali ya sauk'e bindigar daga kan miemie tareda juya baya idanunsa a lumshe.
"Bani nan."hajjo ta buk'ata, babu musu da damk'a mata a hannunta.
Tadubi sojojin da suka tsare miemie tace.
"Zaku iya tafiya." Kana tadubi miemie cikin 6acin rai.
"Meya kawo kinan?"
Miemie da gaba d'aya tsoron PMB ya gama shigarta sai rawar jiki takeyi dakyar ta iya bud'an baki tace.
"Nan ne masauk'ina."tafad'a muryarta na rawa kuka na shirin k'wace mata.
"Banjin nan yayi kama da d'akin ki."hajjo tafad'a tana mata kallon tuhuma.
  Da mamaki miemie take kallonta.
"Amma..."bakinta ne ya tsaya sakamakon k'arewa d'akin kallo datayi, babu shakka nan baiyi kama da masauk'inta saboda kalan d'akin sannan ta zubarda kaya a kan gado,but yanayin d'akin d'aya.
Kallo duka suka bita dashi sa6anin murad daya juya musu baya.
  Hajjo ta dubeta fuskarta expressionless tace
"Nakejin an sanar dake dokokin gidan nan,banyi niyar miki magana ba saboda ganin mutuncinki amma a yanzu kin fara wuce gona da iri,na lura wani abu na yawo akanki tun zuwanki,kin aekata laifi har uku a cikin awanni takwas da zuwanki gidan nan,you're new in this place shiyasa ban miki hukunci ba sannan ina ganin kimarki naganin ke likitan mai martabace,yakamata ki ajiye duk wani rawar kai da rashin hankalinki a gefe ki kula da aekinki,akwai banbanci tsakanin inda kika fito da gidan sarauta,so ki kama kanki inkina so kizauna a cikin gidan nan in ba haka ba ki shirya barin gidannan a kowani lokaci saboda akwai likitoci irinki da dama,na jaddada miki ki rik'e mutuncinki kafun a ga darajarki anan,so is better to stay within your limits." Tana kaiwa nan ta dubi mermu
"Ki kula da wannan saboda gaba ta aekata laifi yana iya shafanki." Tanakai wa nan tasa kai tafita batareda ta dubi halin da PMB ke cikiba zarah da amatullah sukabi bayanta.
Miemie na tsaye ta k'urawa bayan PMB ido tanaso tayi magana ta kasa,bakinza ya gama mutuwa jin maganganun hajjo,tunda take babu wanda ya ta6a zaginta ta kyale sai a yau karon farko data fara gane kuskurenta,ita kanta tasan ta aekata abubuwan da basu daceba a zuwanta,wani hawayen ne yasake bin idanunta.
ManSadi zai yi magana suka tsinkayi muryar murad.
"Gerrout!"yafurta a hankali.
"Yall...
"What the...I said out!"ya maimata idanunsa a lumshe.
Take ManSadi yama mermu alamar ta fita da miemie.
Miemie still tana kallonsa hawaye na zuba a idanunta, jikinta ne yagama sanye takasa tafiya saiji tayi mermu tarik'o hannunta, a hankali ta d'aga kai ta kalleta, lumshe mata idanu tayi alamar kartadamu tazo su tafi, jiki ba lakka miemie tabita tana waiwayen murad da har yanzu bayansa a juye.

SAUYIN RAYUWA (EDITING)Where stories live. Discover now