TAMBAYOYI DA AMSOSHI

3.1K 105 1
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum warahmatullah, Malam don Allah hukuncin macen da ke shayarwa kuma ga karamin ciki akan azumi, ya za ta yi?Allah saka da alkhairi malam.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, Lamarin mai ciki da mai shayarwa game da yin azumi ya rabu gida biyu ne:

1. Duk mai cikin da take da ikon iya yin azumi ba tare  da ta cutu, ko abin da ke cikinta ya cutu ba, to wajibi ne ta ɗauki azumi, idan kuma ta qi ɗauka ta yi laifi matuqar ta san za ta iya yi ba tare da ita ko a abin cikinta sun sami matsala na jigata ko faɗawa mummunan hali ba. Haka nan hukuncin yake ga mai shayarwar da ta san idan ta yi azumi yaronta da take shayarwa ko ita kanta ba za su cutu ba, ita ma idan ta qi ɗaukar azumi tare da ta san za ta iya, to ta yi laifi.

2. Amma duk mai ciki ko mai shayarwar da suka san za su cutu, ko abin da ke ciki ko wanda ake shayarwa su ma za su cutu idan sun yi azumi, to waɗannan suna da azuri idan suka sha azumi, hukuncinsu shi ne rama azumin da suka sha a wasu ranaku na daban a lokacin da dama ta samu a gare su, saboda hukuncinsu dai-dai yake da maras lafiya, saboda ayar Alqur'ani ta bayyana cewa maras lafiya zai rama azumin da ya sha ne a wasu ranaku na daban, kamar yadda ya tabbata a aya ta 184 ta suratul Baqara.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
1/Ramadan/1440 h.
06/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now