*054 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN WACCE ADDU'A CE TA DACE MAI CIKI TA RIQA YI?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum malam, da fatan kana lafiya, dan Allah wace addua mai ciki za ta riqa yi dan fatan Allah ya sauke ta lafiya, kuma Allah ya kawo haihuwa cikin sauki?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam. Ƴar uwa babu wata keɓantacciyar addu'a da na sani da ta tabbata daga manzon Allah s.a.w cewa ita ce mai ciki za ta riqa yi, sai dai Annabi s.a.w ya koyar da addu'o'i da suka qunshi neman yaye duk wata damuwa, da cuta da ke damun ɗan'adam, daga cikin waɗananan addu'o'i akwai addu'ar da Annabi s.a.w ya koya wa Usman ɗan Abu Áss a lokacin da ya kai masa koken wani ciwo da ke damunsa a jikinsa tun lokacin da ya Musulunta, sai Annabi s.a.w ya ce masa ya sanya hannunsa a daidai inda yake masa raɗaɗi a jikin nasa, sannan kuma ya yi Bismillah sau uku, sannan sai ya karanta wannan addu'ar sau bakwai:
“A'UZHU BILLAHI, WA QUDRATIHI MIN SHARRI MA AJIDU WA UHÁZHIRU”.
(أَعُوذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وَأُحَاذِرُ).
Ma'ana:
Ina neman tsarin Allah da ikonsa daga sharrin abin da nake ji (a jikina), kuma nake tsoro. Muslim 2202.
Bayan wannan za ki iya haɗawa da "Hasbiyallahu Wa Ni'imal Wakeel", da Fatiha da sauran duk addu'o''in da za ki iya da Hausa ko da Larabci a kan Allah ya sauke ki lafiya, in Allah ya so za ki ga ikon Allah, da taimakonsa, kuma kina iya maimaitawa lokaci bayan lokaci.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
28/5/1440 h.
03/02/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Storie brevi*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: