*JANABA TA SAME NI, BAN YI WANKA BA SAI HAILA TA ZO MINI, YA ZAN YI WAJEN YIN WA

538 10 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*JANABA TA SAME NI, BAN YI WANKA BA SAI HAILA TA ZO MINI, YA ZAN YI WAJEN YIN WANKA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam. Dan Allah tambaya ta ita ce, malam idan mutum yana da janaba ajikinshi bai yi wanka ba sai haila ta same shi ya xai yi wajan yin wankan su? nagode   Allah ya kara basira ameen.

AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa idan abubuwa guda biyu masu wajabta wanka suka haɗu a lokaci ɗaya, kamar janaba da haila, ya halasta a yi niyyarsu duka da wanka ɗaya, wato a yi wanka ɗaya da niyyarsu duka. Wannan shi ne fahimyar mafi yawan ma'bota ilimi da suka haɗa da Aɗá'u da Abuz Zinad da Rabee'a, da Malik da Sháfi'iy da Ishaq da As'háburra'ayi. Duba Almugniy na Ibn Qudama 1/162.

Amma idan janaba ya sami mai haila za ta iya yin wanka da nufin gusar da janaba, tare da cewa hailarta tana nan, saboda ta sami damar karanta Alqur'ani, domin janaba tana hana taɓan Alqur'ani da karanta shi, ita ko haila tana hana taɓan Alqur'ani ne kawai ba tare da hana karanta shi da ka ba, saboda haka za ta iya yin wankan janaba don ta fa'idantu da karanta Alqur'ani da ka, ba tare da ta taɓa shi ba.
Shi wankan yana gusar mata da janaba ne kaɗai ban da haila ɗin, kamar yadda Ibnu Qudama ya faɗa.
Duba Almugniy 1/154.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
10/6/1440 h.
15/02/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now