SHIGA MASALLACI DA JANABA*

307 1 0
                                    

*Tambaya ta 118*

*SHIGA MASALLACI DA JANABA*

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,

Ko ya halatta mai janaba ya shiga masallaci, ko ya yi karatun Alqur’ani, ko ya ɗauki Alqur’anin?

AMSA A118:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] Malamai sun saɓa wa juna a kan waɗannan abubuwa guda uku: Waɗansu sun hana mai janaba da mai haila karatun Alqur’ani, ko ɗaukar mus-hafin Alqur’anin, ko kuma zama a cikin masallaci. Waɗansu kuma sun halatta masu yin waɗannan abubuwan. Matsayin da waɗannan na-ƙarshen su ke kai kuma shi ya fi daidai, saboda dalilai guda biyu, kamar haka:

(i) Dalilan da malaman farko suka kawo domin tabbatar da hukuncin ba su inganta ba:
Hadisin da Abu-Daawud (229) da At-Tirmiziy (146) da An-Nasaa’iy (1/144) da Ibn Maajah (594) suka riwaito daga Aliyyu (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

كَانَ رَسُولُ الله – صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ – لَا يَحْجِزُهُ شَيْءٌ مِنَ الْقُرْآنِ لَيْسَ الْجَنَابَة
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance babu wani abin da ke tsare shi daga Alqur’ani in dai ba janaba ba.

Ahmad da Al-Albaaniy sun raunana wannan hadisin.
(Dubi Tamaamul Minnah, shafi: 119).

Al-Imaam As-Shawkaaniy (Nailul Awtaar: 1/284) ya ce: ‘A cikin wannan babu wani abin da ke nuni ga haramci; matuƙar abin da ke cikinsa kawai shi ne: Ya daina karatun ne a halin janaba. Wannan kuwa bai isa ya zama dalili a kan karhanci ba ma, to ta yaya kuma za a kafa dalili da shi a kan haramci?!!’

(ii) Ƙa’idar da malaman Usuul suka shimfiɗa na Baraa’atul Asliyyah: Watau tabbatuwan rashin hukunci a kan kowane abu har sai an samu dalilin da ya tabbatar da shi, shi ne asali a wannan wurin. Don haka, ya halatta mutum musulmi ya karanta Alqur’ani ko da kuwa bas hi da tsarki, har sai lokacin da aka samu sahihin dalili a fili ƙarara da ya hana.

Malamai sun yarda cewa, ko da take ba a haramta wa mai janaba da mai haila yin karatun ba, amma dai abu ne mai kyau mai janaba ya gaggauta yin wanka kafin ya yi karatun, saboda hadisi sahihi da Abu-Daawud (17) da An-Nasaa’iy (1/37) da Ibn Maajah (350) suka riwaito daga maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

إِنِّي كَرِهْتُ أَنْ أَذْكُرَ اللهَ إِلَّا عَلَى طُهْرٍ
Ni, ina ƙyamar in ambaci Allaah sai dai a cikin tsarki.
(Dubi Tamaamul Minnah: 1/110).

[2] Game da ɗaukar Alqur’ani kuwa, kodayake hujjojin sun inganta ta fuskar isnadi, amma kuma ta fuskar kafa hujja ba su inganta ba, in ji malamai:

(i) Don haka, ba daidai ba ne kafa hujja a nan da maganar Allaah Ta’aala:

ﭽ ﭙ  ﭚ  ﭛ        ﭜ  ﭝ  ﭼ
Babu mai shafarsa sai dai tsarkaka
(Surah Al-Waaqi’ah: 79)

Domin abin nufi da shi a nan shi ne: Lauhul-Mahfuuz, watau: Babu mai shafar Lauhul-Mahfuuz sai dai Mala’iku. Domin kuma shi ake nufi da: Kitaabul-Maknuun a ayar da ke saman wannan.

(ii) Haka kuma hadisin da Maalik (1/199) da Ibn Hibbaan (469) da Ad-Daaraqutniy (1/122) suka riwaito kuma Al-Albaaniy (Al-Irwaa’u: 122) ya inganta shi cewa:

لَا يَمَسُّ الْقُرْآنَ إِلَّا طَاهِرٌ
Kar wani ya shafi Alqur’ani sai mai tsarki

Ingantacciyar fassara a wurin malamai ita ce: Kalmar Taahir, watau Mai Tsarki kalma ce ‘mushtarakah’ da take ɗaukar fassara ko ma’anoni masu yawa. Amma dai abu ne sananne cewa: Musulmi a duk inda ya ke mai tsarki ne: Ko yana da janaba ko haila, ko bashi da su. Domin maganar Allaah Ta’aala cewa:

ﭽ  ﭢ  ﭣ   ﭤ ﭼ
Kadai su mushirikai najasa ne
(Surah At-Taubah: 28)

Sannan kuma da maganar da Al-Bukhaariy (283) ya riwaito da isnadinsa cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya gaya wa Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

« سُبْحَانَ اللَّهِ ، إِنَّ الْمُؤْمِنَ لاَ يَنْجُسُ »
Subhaanal Laah! Ai mumini ba ya najastuwa!

Don haka, a nan ba za a haramta wa musulmi shafa ko ɗaukar Alqur’ani ba, ko da kuwa yana da janaba ko tana da haila ko nifasi, har sai lokacin da aka samu dalili sarihi a fili ƙarara, wanda kuma ba ya ɗaukar wani tawili, da ya haramta hakan.
[3] Maganar zama a cikin masallaci shi ma dai kamar haka ɗin ne. In ba an samu dalili sahihi kuma sarihi mai hanawa ba, to kuwa ba za a hana musulmi mai janaba ko mai haila shiga da zama a cikinsa ba.

(i) Domin tun da dai ga kafirai da mushirikai a zamanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) suna shiga masallacinsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) su yi masa tambayoyi, su tattauna da shi, kuma har da wanda ma aka taɓa ɗaure shi daga cikinsu a cikin masallacin kwana da kwanaki, ai wannan kaɗai ma ta isa hujja. Domin kamar yadda kowa ya sani, duk rashin tsarkin musulmi bai kai rashin tsarkin kafirai da mushirikai ba! Sannan kuma a duk faɗin duniya, babu wani masallacin da ya kai daraja da alfarmar masallacinsa (), in ban da Masallacin Harami na Birnin Makkah.

(ii) Sannan kuma ga Sahabbai da yawa Ahlus-Suffah a zamaninsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) waɗanda suke kwana da tashi a cikin masallacinsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Kuma sanannen abu ne cewa ana samun masu yin mafarki a lokutan barcinsu, amma kuma ba a taɓa ji ko ganin wanda aka hana shi shiga ko cigaba da zama a cikin masallacin ba. Sannan kuma akwai wata baƙar macen da ta musulunta kuma aka yi mata tanti a cikin masallacin, kuma abu ne sananne cewa mata suna haila, amma ba a ji inda aka hana ta zama a cikin tantinta ba a lokacin al’adarta. (Dubi: Al-Muhallaa).

(iii) Amma kafa hujja da ayar da ta ce:

ﭽ ﮣ  ﮤ  ﮥ  ﮦ  ﮧ  ﮨ    ﮩ  ﮪ  ﮫ  ﮬ  ﮭ  ﮮ  ﮯ  ﮰ  ﮱ       ﯓ    ﯔ  ﯕ  ﯖﯗ ﭼ
Ya ku waɗanda suka yi Imani! Kar ku kusanci sallah a halin kuna cikin maye, har sai kun san irin abin da kuke faɗi. Haka kuma a halin kuna da janaba – sai dai masu ƙetare hanya - har sai kun yi wanka.
(Surah An-Nisaa’i: 43)

Fassararta, kamar yadda Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) ya riwaito shi ne: Matafiya ne da janaba ta same su, sai su yi taimama su yi sallah. (Tamaamul Minnah: 1/112).

(iv) Haka kuma hadisin da ya ce:

إِنِّي لَا أُحِلُّ الْمَسْجِدَ لِحَائِضٍ ، وَلَا لِجُنُبٍ
Ni dai ban halatta masallaci ga mai haila da mai janaba ba

Wannan hadisin da Abu-Daawud (232) da wani irinsa da Ibn Maajah (645) suka riwaito shi, malaman hadisi sun tabbatar da cewa mai rauni ne, saboda mudtarib ne, kuma akwai wata Jasrah Bint Dajaajah a cikin isnadinsa, wadda kuma  Al-Bukhaariy ya raunata ta. Ita kuwa riwayar Ibn Maajah malamai sun tabbatar cewa mursalah ce.

(v) Sai dai kuma duk lokacin da mai janaba ko mai haila ke son zama a cikin masallaci, to mustahabbi ne su yi alwala. Sa’eed Bn Mansuur (646) ya riwaito atharin da malamai suka hassana shi cewa: Haka Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) suka kasance suna aikatawa. (Dubi: Tamaamul Minnah: 1/112).

Wannan shi ne jawabinmu a kan wannan fatawa, a taƙaice.

Wal Laahu A’lam.

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
5/8/2019
3: 05pm.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now