*TAMBAYA TA 016:*
*HOTON MAMACI A ‘SOCIAL MEDIA* ’
_As Salamu Alaikum Wa Rahmatul Laahi Wa Barakatuh_ .
Da fatan malam yana lafiya.
_Please,_ malam ko ya halatta a sa hoton mamaci a _profile_ ko _status?_
*AMSA: A016:*
_W alkm slm w rhmtul Laah w brktuh._
Abin da Malamai suka tabbatar a nan shi ne: Idan dai ba da larura (kamar na _passport_ don shiga makarantu, ko neman aiki, ko fita ƙasashen waje, da makamantansu) ba, musulmi ba ya yin harka ko mu’amala da hotuna na abubuwa masu rai (kamar mutum, ko mala'ika, ko dabba, ko tsuntsu, ko ƙwaro da sauransu), kuma ko masu inuwa ne (kamar sassaƙaƙƙu ko ginannu da laka, ko roba, ko siminti), ko marasa inuwa (kamar waɗanda aka zana da hannu, ko aka ɗauka da kyamara). Saboda irin kausasa magana da tsawa mai tsanani da shari’a ta yi a kan haka:
[1] Abu ne sananne cewa: Hotuna su ne dalilin farko na kaucewa ko karkacewar mutane daga kan hanyar Allaah tun a zamanin Annabi Nuhu _(Alaihis Salaatu Was Salaam)._ Mutanen zamaninsa su ne suka sassaƙa hotunan manyan malamansu domin tunawa da su a farko, amma daga baya sai suka zama abubuwan bauta ba Allaah ba!
Daga ƙarshe kuma da aka turo Manzon Allaah Mai wa’azi na farko a duniya: Annabi Nuhu _(Alaihis Salaam)_ domin ya hana su, sai kawai suka kangare kuma suka taurare, har ma suka riƙa faɗa wa mutanensu, kamar yadda Allaah Ta’aala ya ambato daga gare su cewa:
وَقَالُوا لَا تَذَرُنَّ آلِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا
Kuma suka ce: Kar ku yarda ku rabu da abubuwan bautarku: Kuma kar ku rabu da Waddu da Suwaa’u da Yaguuthu da Ya’uuqu da Nasru.A ƙarshe ƙissar dai hallaka ce ta same su, kamar yadda Allaah ya ce:
مِمَّا خَطِيئَاتِهِمْ أُغْرِقُوا فَأُدْخِلُوا نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا لَهُمْ مِنْ دُونِ اللَّهِ أَنْصَارًا
Saboda irin laifuffukansu sai aka nutsar da su a cikin ruwa, kuma aka shigar da su cikin Wuta, kuma ba su samu wani mataimaki ba a bayan Allaah.[2] Sannan a cikin Hadisai sahihai Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya yi tsawa a kan al’amuran hotuna, kuma bai bambance ba a tsakanin nau’ukansu, kamar inda ya ce:
أَشَدُّ النَّاسِ عَذَاباً الَّذِينَ يُضَاحُونَ بِخَلْقِ اللهِ
Mafiya samun tsananin azaba daga cikin mutane su ne: Waɗanda suke kwaikwayon halittar Allaah.Haka kuma inda ya ce:
أَشَدَّ النَّاسِ عَذَابً يَوْمَ الْقِيَامَةِ الْمُصَوِّرُونَ ، يُقَالُ لَهُمْ أَحْيًون مَا خَلَقْتُمْ
Mafiya samun tsananin azaba daga cikin mutane a Ranar Ƙiyamah su ne: Masu yin hotuna, za a ce da su: Ku raya irin abubuwan da kuka halitta.[3] Don haka, ba daidai ba ne musulmi ya riƙa amfani da hotunan mutane (rayayyu ko matattu, manya ko yara, kuma maza ko mata, haka ma sauran dabbobi ko tsuntsaye da sauransu), a cikin ‘ _social media’_ kamar yadda aka bayyana a cikin tambayar, ko kuma a wani wurin da ba wannan ba, in dai ba da wata larura mai ƙarfi irin wanda Shari'a ta amince ba.
Maimakon haka sai ya yi amfani da hotunan abubuwan da ba masu rai ba, kamar itatuwa, ko furanni, ko duwatsu, ko rana, ko wata, ko sararin sama, ko rafuka, ko teburori, ko kujeru, ko gidaje, ko motocci, ko jirage, da sauran irinsu.
_Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: