*030 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN JANABAR WANDA TA YI INZALI TA HANYAR HARAM*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahmatullah. Malam barka da warhaka, Malam ina da tambaya kamar haka: WAI DOLE NE IDAN AKA SAMU MATSALA NAMIJI WANDA BA MUHARRAMIN MACE BA YA TABA TA SAI TA YI WANKA KOKO?
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah. Irin wannan aiki haramun ne, mu ji tsoron Allah a cikin dukkan al'amuranmu, kuma mu guji duk wani yanayi da zai sa mu ƙaɗaita da wanda ba muharramunmu ba, saboda hadisin da Bukhariy ya ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas, Annabi s.a.w ya ce: "Kada wani mutum ya keɓanta da wata mace face sai da muharraminta". Bukhariy 5233.
Ƴar uwa lallai babu bambanci a tsakanin mace ko namijin da suka yi inzali (fitar da maniyyi) ta hanyar haram ta fuskar wajabcin yin wankan janaba. Inda suka bambanta shi ne, mutumin da ya fitar da maniyyi ta hanyar halas, ana sa ran zai sami ladar yin wankan janaba, amma wanda ya yi wanka ta dalilin janaba ta hanyar haram, wannan ya dai yi tsarki kawai, saboda ba ta hanyar halas janabar ta same shi ba, kuma wajibi ne ya yi wannan tsarkin saboda samun damar ci gaba da ibada.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
7/5/1440H.
13/01/2019 m.
![](https://img.wattpad.com/cover/186935965-288-k193559.jpg)
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: