*MIJINA YANA SADUWA DA NI TA DUBURA!*
Assalamu alaikum warahmatullah wabara katuhu
Tambaya
Amma dan Allah ina bukatar ku ɓoyeI'D ɗina
saboda kare mutunci na da na mijina.
Yau shekarar mu ɗaya da 'ƴan watanni kenan
da yin Aure mu..,
Akoda yaushe Mijina yafi son yin
Jima'i dani ta baya. wai acewar sa yafi jin daɗi
kuma buƙatar shi tafi biya.,
Naje wajen wata walimar ƙawata naji wani
Malami da aka gaiyaceshi yin wa'azi yace ba
Kyau yi ta baya..
Koda nasanar wa Mijina yace wai in Rabu
dasu Ƙarya sukeyi ai ance Matarka gonarka ce
ka shigeta duk ta inda kake so.
TO DON ALLAH YAYA LAMARIN YAKE???
AMSA
====Waalaikumussalam warahmatullah wabara katuhu
Yadda lamarin yake, Idan Saduwar da kukeyi
ta dubura ne, to Wannan HARAMUN NE.Saboda Allah ya sanya mana dalilin Saduwar
Jima'i abisa manufofi ne guda biyu.1. Na Farko domin samar da zuriyyah
Halastacciyya. shi yasa ma Allah (swt) yace
MATAYENKU GONAKINKU NE.
Abinda Ake nufi anan Farjinsu shine Gonar da
ake yin shukar aciki.
Maniyyin mazaje shine IRIN DA AKE SHUKAWA.
'YA'YAN Da aka haifa sune AMFANIN GONAR.
Don haka be halatta ayi Jima'i ta dubura ba
saboda Dubura BA WAJEN DA AKE DAUKAR CIKI
BANE.. Kuma duburar Dan Adam anyita ne
domin fitar da Ba-haya, ba domin Jima'i ba.
Allah yana cewa : "KUZO MUSU TA INDA ALLAH
YA UMURCE KU"
Shi kuwa Allah ya umurce mazaje nesu sadu
da matayensu ta farjinsu ba ta dubura ba.2. Dalili na biyu na saduwar Jima'i shine
domin Abiya wa juna bukatarsu ta jinsi da
jinsi.
Ita kuwa saduwa ta dubura ba zata gamsar
da matar ba. ko da shi mijin yana jin cewar ya
gamsu.
Wasu malaman ma sunce dalili daya ne yake
sa asadu da mace: don haifar da zurriyya ba
wai don biyar bukata ba kadai.
Abinda yake Halastacce shine: Miji zai iya
saduwa da matarsa ta baya, AMMA TA CIKIN
FARJINTA BA TA DUBURA BA..Wannan halal ne.
Annabi (saww) yace: "DUK WANDA YA SADU DA
MATARSA TA DUBURA TSINANNE NE".
(Abu dawud da Nisa'iy ne suka ruwaito shi.
kuma Sahihi ne Ligairihi).
An ruwaito wannan hadisin ta hannun
Sahabbai masu yawa sosai. acikinsu akwai:
Sayyiduna Aliyyu bn Abi Talib (ra).
* Abu Hurairah
* Umar bn Alkhattab.
* Talqu bn 'Aliyyin
* Khuzaymah
* Aliyyu bn Talqin.
* Ibnu Mas'ud.
* Ibnu Abbas.
* 'Uqbatu bn Aamir.
* Jabir bn Abdillah.
* Albarra'u bn Aazib.
* Abdullahi bn 'Amr
* Anas bn Malik.
* Abu Dharrin Al_Giffary (Allah ya yarda dasu).
Duk da cewa akwai kalamai akan hanyoyin
hadisan, Amma kuma hanyoyin suna Qarfafar
Junansu.
Wannan Ayar wacce mijin naki ya dogara da
ita, (Ku zowa gonakinku ta yadda ku ka so).
Ki gaya masa be fahimci ayar bane. kuma be
san dalilin saukarta bane. domin kuwa ayar
tana nufin cewar -
"Ku sadu da matayenku Akwance, koatsaye,
ko a tsugunne, ko azaune, kota gaba ko ta
baya, AMMA TA FARJINSU.. BA TA DUBURA BA.
Shi yasa ma daya ayar take cewa: "KU ZO
MUSU TA WAJEN DA ALLAH YA UMURCE KU".
Ayar ta sauka ne yayin da wasu Sahabbai
suka tambayi Manzon Allah(saww) akan wata
maganar da sukaji awajen Yahudawa. wai
Idan mutum ya sadu da matarsa ta baya
Amma ta farjinta, Idan ta samu ciki ahaka, wai
Za'a haifi yaron da Juyayyen idanu (Harara-
Garke).
Don haka Allah ya saukar da Ayar domin ya
Qaryata maganar Yahudawa.
Ki gaya masa Cewar Dukkanin Maluman
Maz_habobin nan hudu da ma wasunsu Sunyi
ittifaqi akan haramcin saduwa ta dubura gaba daya.
Ki gaya wa Mijinki cewar Idan be dena ba,
WALLAHI MANZON ALLAH (SAWW) YACE:
"DUK WANDA YAYI JIMA'I DA NAMIJI, KO KUMA
YA SADU DA MACE TA DUBURARTA, ALLAH BA
ZAI DUBESHI DA RAHAMA BA".
YA ALLAH KA TSAREMU KA KIYAYEMU.
AAAAMEEEEEN.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: