*TAMBAYA TA 027*
*CINIKIN ZINARE TA YANAR-GIZO*
_As Salamu Alaikum._
Menene hukuncin wanda yake mu’amala da swissgolden: Idan ya sa *100k* sai bayan watanni biyu a ba shi *180k* . Ya halatta ko bai halatta ba? Harkar saye da sayar da zinare ake yi.
*AMSA A027:*
_W alkm slm w rhmtul Laah._
A nan kafin a samu cikakkiyar amsa ya kamata a samu gamsassun amsoshin waɗansu tambayoyi kamar haka:
(1) Waye, ko su waye *swissgolden?*
(2) Ina ne asalinsu da tushensu?
(3) Meye manufofinsu?
(4) Kafaffu ne a ƙasa?
(5) Hukuma ta san da zamansu?
(6) Suna da rajista da Gwamnatin Jiha ko ta Tarayya?
(7) An tabbatar su ba ɗaya daga cikin ƙungiyoyin *419* ba ne?
(8) Wace irin harkar saye da sayar da zinaren suke yi?
(9) A wurin waye suke saye, kuma wa suke sayar wa da zinaren?
(10) Suna kiyayewa a kan ƙa’idojin shari’ar musulunci game da cinikin zinare?
(11) An tabbatar na’ukan riba na jinkiri da riba na ƙari ba su shiga cikin harkar?
(12) Sannan riba kaɗai ake samu a cikin harkar, ba a faɗuwa?
(13) Da gaske *80k* da aka ba shi bayan watanni biyu shi ne haƙiƙanin rabonsa?
(14) Ta yaya zai tabbatar ba a cuce shi ba, kuma shi bai yi cuta ba?
(15) Wannan bai yi kama da cinikin *Gharar* (watau: cinikin biri a sama) da Musulunci ya hana ba?!
(16) Anya wannan ba wani nau’in cinikin _‘pyramid’_ ne da Malamai suka hana ba?
(17) Watau: Inda ake amfani da ajiyan sababbin _‘members’_ don cigaba da azurta tsofaffi?
In ana da tabbaci ko ana shakka game da sahihancin wannan harkar, to gara musulmi ya nisance ta, saboda maganar Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ cewa:
دَعْ مَا يُرِيبُكَ إِلَى مَا لَا يُرِيبُكَ
Ka rabu da abin da kake kokwanto, zuwa ga abin da ba ka kokwantonsa._Wal Laahu A’lam._
*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
13 – 03 - 2018
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Cerita Pendek*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: