*ƘASARU A GARIN DA BA NASA BA

80 1 0
                                    

*TAMBAYA TA 127*

*ƘASARU A GARIN DA BA NASA BA*

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,

Na samu aiki ne a wani garin da ba nawa ba na tsawon shekara ɗaya, to ina hukuncin yin ƙasaru a kaina?

AMSA A127:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Amsar irin wannan tambayar ya gabata a amsar tamabaya ta A007 wanda wata mace ta aiko kuma aka rubuta amsar a ranar 23/1 2018 cewa:

Ana yin ƙasaru ne a cikin halin tafiya, ko kuma a cikin halin da matafiyi bai rabu da larurar tafiyar ba.  Watau kamar a halin da yake zaune a wani wurin da ba garinsa ba, a cikin hali ko yanayi na rashin natsuwa irin na mazaunin gida.

Don haka, a duk lokacin da kika samu kanki a cikin halin da ba za a kira ki mai tafiya ba, ko a Abuja ne ko a Zariya ne ko kuma ma a wani wurin ne, to ba za ki yi ƙasarun Sallah ba.

Sannan kuma ko da kina cikin halin tafiyar sai kuma kika yi Sallah a bayan limamin da yake cika Sallah, to sai ki cika sallarki tare da shi, in ji waɗansu malaman.

Amma a wurin waɗansu malaman kuma, waɗanda suke ganin yin ƙasarun wajibi ne ba Sunnah ko mustahabbi ba, sun tsaya kan cewa, ko a wannan halin na sallah a bayan limami mazaunin gida ma ƙasarun dai za ki yi.

Wal Laahu A'lam.

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
23 - 8 – 2019

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now