*_LOKACI MAFI TSADA NA KARANTA ALQURANI A RAMADHANA_*
Karanta alqurani acikin Daren watan Ramadhana shine mafi alkhairi da falala fiye da karanta shi a yinin Ramadhana,musamma dararen goman karshe na Ramadhana.
Domin:~
☆Manzon Allah s.a.w da Mala’ika Jibrilu suna yin Darasin Alquranine a dararen Ramadhana ba yininsa ba.☆Shi kansa Alqurani yana kafa hujja na neman citon bawane awajan Allah da cewa na hanashi barci saboda yawan karantani da yàke acikin dare,sai yace ya Allah ka bani cetonsa.
☆Alquranin kansa an saukar da shine acikin daren lailatul Qadri daga Lauhul Mahfuz zuwa baitun izza a saman duniya kamar yanda Ibn Abas R. A ya fada.
☆Mafi yawan sahabban Manzon Allah s.a.w da Tabi’ai da sauran Magabata na kwarai sunfi yin tilawar alqurani a watan Ramadhana ne da dare.
☆Sannan tilawar da dare yafi samun ikhlasy da kyakkyawar niyya da kuma nesa da riya da son nuna yawan ibada.
☆Sannan da dare anfi samun nutsuwa da nishadi na karatun alqurani sannan babu saurin gajiya da kasala.
☆Sannan yinsa daren yana sanyawa mutum ya dace da daren lailatul Qadri wanda ibada acikin wannan daren daya tafi alkhairi akan ibada a dararen watanni dubu wanda babu daren lailatul Qadri acikinsa.
☆Sannan akarshen kowane dare Allah yana saukowa samar duniya dan amsa addua da tuban bayinsa,sai kuma Allah ya sameka mutane suna barci kai kuma kana tilawar Maganarsa.mi yafi wannan alkhairi ga dan adam.
Yan uwa kada muyi barci mutashi mu rumgumi karatun alqurani mai girma a sauran dararen Ramadhana da dukkan sauran darare baki daya ko mum sami ceton Alqurani mai girma da falala da darajoji masu yawa.
Amma mu sanya ikhlasy acikin Karantun mu.
_Mu sanya koyi da sunnah acikin karatun mu domin Allah baya karbar Wata ibada sai idan anyita dan shi kadai kuma anyita abisa koyi da Manzon Allah s.a.w_
Allah ne mafi sani.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: