*220 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*TA YAYA ZAN GYARA ZUCIYATA DAGA NUFIN AIKATA ZUNUBAI?*
TAMBAYA:
Assalamu aleikm malam, ina yini, malam ina so dan ALLAH kou yi min bayani idan moutoun ya ga zouchiyarsa ta zama da douhou, ma'ana ta fi son saba ma ALLAH a kan biyayya a gare shi wache hanya ya kamata ya bi don samoun haske na zouchi?
AMSA:
Wa'alaikumus salam, duk zuciyar da ta fi son karkata wurin saɓon Allah fiye da yi masa biyayya, to wannan zuciya tabbas ta gurɓace, kuma alama ce da ke nuna mai wannan zuciya yana cikin waɗanda Allah bai yarda da abin da suke yi ba, muna fatan Allah Ta'ala ya kare mu da aikata mummuna, ya ba mu ikon bin umurninsa. Daga cikin hanyoyin da mutum zai bi don kyautata zuciyarsa ta zamo mai son Allah da yi masa biyayya sun haɗa da:
1. Komawa zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki ta hanyar yawan roqonsa a kan ya karkatar da zuciyarsa daga aikata saɓo.
2. Mutum ya yaqi zuciyarsa, ya cire mata shakku, da matsa mata wajen ganin ta yi wa Allah biyayya (wato ya tsarkake zuciyarsa kenan).
3. Yawan tunawa da tsananin azabar da Allah ya tattalar ma da wanda ya aikata saɓon Allah.
4. Mutum ya riqa tuna cewa duk abin da yake yi Allah na kallonsa a duk inda yake, kuma ba abun da zai ɓuya wa Allah game da shi.
5. Tuna cewa mutuwa za ta iya riskar mutum a daidai lokacin da yake aikata wannan saɓo, to mai zai ce wa Allah idan haka ta faru?
6. Yawan tuna kyakkyawar sakamakon da Allah ya tattalar ma da mutanen kirki da suka yi masa biyayya, wanda masu saɓo ba za su sami wannan ba.
7. Mutum ya yawaita zama tare da mutanen kirki, masu yawaita biyayya ga Allah. Da nisantar mutanen banza, da yawan kaɗaita a inda mutanen kieki ba sa ganinsa.
Da ikon Allah Allah zai sa zuciyar bawa ta gyaru idan ya zamo mai kamanta waɗannan abubuwa. Allah ya shiryar da mu.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
18/09/2019 M.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: