*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*MATAR DA KE HAILA SAU BIYU A WATA YA IDDARTA ZA TA KASANCE?*
TAMBAYA:
Salamun alaikum, malam tambayata ita ce, matar da take haila sau biyu a wata ya iddarta take?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Matar da take haila sau biyu a wata iddarta za ta iya kammaluwa a cikin qasa da wata biyu kenan kamar yadda malaman Fiqhu suka tabbatar, saboda Imamu Ahmad ɗan Hambal yana da fahimtar cewa qarancin lokacin tsarki daga haila zuwa haila kwana goma sha uku ne, yayin da kuma Imamuna Maliku da Imamut-Thauriy da Imamus-Sháfi'i da Imamu Abu Haneefa suke da fahimtar cewa qarancin lokacin tsarki daga haila zuwa wata hailar shi ne kwana goma sha biyar. Haka nan kuma malamai sun ce qarancin lokacin haila shi ne yini ɗaya da kwana ɗaya.
Wannan sai ya nuna cewa wata macen za ta iya yin haila biyu a wata ɗaya. Idan mace mai idda ta yi iqrarin ta yi jinin haila uku mabambanta a wata ɗaya, malamai sun ce za a nemi shaidar haka daga makusantanta mata waɗanda aka san su da gaskiya da amana, idan sun ba da shaida a kan haka, to shi kenan za a gasgata ta, kamar yadda ya faru a tsakanin Sayyiduna Aliyu R.A lokacin da wata mata ta kawo masa qara.
Saboda haka, macen da take yin haila biyu a wata ɗaya, da zarar ta yi haila sau uku, wato haila biyu a wata ɗaya, sai kuma cikon na ukun a watan da ke biye masa, to shi kenan iddarta ta qare.
Don ganin waɗannan bayanan, duba ALMUGNIY 1/225.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
3/8/1440 h.
09/04/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Krótkie Opowiadania*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: