SHIN YA HALATTA NA YI AIKI DA N.G.OS ?

184 0 0
                                    

*SHIN YA HALATTA NA YI AIKI DA N.G.OS ?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum, Allah ya taimaki Dr. Don Allah Dr. Ya halatta mutum yayi aiki da 'yan N.G.Os?

*Amsa*

Wa alaikumus Salam
Mutukar babu haramun a cikin aikinsu ya halatta ko da kuwa kafurai ne.
Annabi (SAW)  ya yi Mu'amala da Yahudawa kuma ya mutu ya bar jinginar silkensa na yaki a wajan Bayahude kamar yadda maruwaita hadisi suka yi bayani.

Duk N.G.O din da aka san mugunyar manufarsu ga Addini ko ga mutanen da suke yiwa aiki, bai halatta ayi aiki da su ba.
Tsarkake abinci yana daga cikin dalilan amsar addu'a kamar yadda hadisai suka tabbatar.

Allah ne mafi sani.

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

01/08/2019

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now