*SHIN ANA YIN ZAKKAR FIDDAKAI DA KUDI, KUMA WA YA KAMATA NA BA?*

235 6 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*SHIN ANA YIN ZAKKAR FIDDAKAI DA KUDI, KUMA WA YA KAMATA NA BA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum,  malam tambayata ita ce mutum zai iya ba wa dan uwansa zakkar fiddakai wadda suke uwa daya uba daya, sannan kuma dan Allah a temakemu a duba mana in mutum zai ba da fiddakai na kudi nawa ne kowane mutum daya zai bayar?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, dama ita zakkar fiddakai an shar'anta a ba wa talakawa ne, saboda haka matuqar wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya da shi ɗin nan yana daga cikin faqirai ko miskinai, to ya halasta ki ba shi zakkar fiddakai, kawai sharaɗin dai ya zamana wanda za a ba zakkar yana daga cikin faqirai ko miskinai, kamar yadda malamai suka tabbatar.

Shi ko hukuncin yin zakkar fiddakai da kuɗi, malaman Musulunci suna da fahimta guda biyu: na farko suna ganin ya halasta mutum ya yi zakkar fiddakai da kuɗi, saboda su a fahimtarsu daga cikin manufar shar'anta zakkar fiddakai shi ne don a faranta wa talakawa rai a ranar Idi, saboda haka suke da fahimtar za a iya ba da kuɗin da zai yi dai-dai da qimar sa'i ɗaya na abinci, masu wannan fahimtar sun haɗa da: Imam Abu Haneefa, da Hasanul Basriy, da Umar ɗan Abdul'aziz, da Thauriy. Amma Is'haq da Abu Thaur sun ce qimar zakkar fiddakai ba ya isarwa a yi da kuɗi har sai in akwai lallura.

Amma fahimtar mafi yawan malaman Musulunci ita ce: Qimar Zakkar fiddakai da kuɗi ba ya isarwa kamar yadda Imam Malik, da Imam Ahmad, da Ibn Munzhir suka faɗa.

Duba ALMAJMU'U 6/144 na Imamun Nawawiy.

Saboda haka, abin da ya fi cancanta shi ne a fitar da zakkar fiddakai da nau'in abincin da aka fi ci a garin da mutum yake, sai idan akwai lallura ne sannan a ba da kuɗin da ya yi dai-dai da qimar sá'i ɗaya na abinci.

Sai dai fa ni ban san ko nawane qimar kuɗin zakkar fiddakai a kuɗin qasarmu ba, saboda ni da abinci nake yi ba da qima na kuɗi ba, abin dai da ya wajaba a kiyaye shi ne: Asali dai kowane mutum ɗaya da zai yi fiddakai zai ba da abinci ne SÁ'I ɗaya, sá'i ɗaya kuma shi ne Muddun Nabiyyi huɗu.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
5/Ramadan/1440 h.
10/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now