WAI BA SAKI UKU YAKE NUFI BA!*

128 0 0
                                    

*Tambaya ta 111*

*WAI BA SAKI UKU YAKE NUFI BA!*

_Assalaam Alaikum,_

Miji ne ya ba matarsa takardar saki ɗaya, aka daidaita su ta koma. Sai suka sake samun matsala, ya sake sakin ta a gaban jama’a saki-uku. Daga baya kuma sai yake neman ta dawo da hujjar cewa wai ba uku ya yi nufi ba. Ya faɗi ukun a lokacin ne domin wai kar a tilasta shi ya mayar da ita. Ina matsayin wannan auren?

*AMSA A111:*

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh_ .

[1] Da farko dai dole mu san cewa: Ba a wasa da saki a musulunci. Don haka, duk wanda ya saki matarsa da ba’a ko da wasa ba da gaske ba, to sakinsa dai ya tabbata. Annabi _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ ya ce:

ثَلَاثٌ جِدُّهُنَّ جِدٌّ وَهَزْلُهُنَّ جِدٌّ : النِّكَاحُ وَالطَّلَاقُ والرَّجْعَةُ
Abubuwa uku yin su da gaske ko da wasa duk da gaske ne: Ƙulla aure da sakin aure da mayar da aure.
_Sahih Abi-Daawud: 1920_ .

[2] Abu na-biyu, lallai mu san cewa: Wanda sakin aurensa yake inganta shi ne: Miji, baligi, mai hankali, kuma mai zaɓin ransa. Don haka, duk wanda ba shi da zaɓin ransa, kamar wanda aka tilasta masa, ko mai maye, ko ruɗaɗɗe, ko wanda yake cikin matsanancin fushimalamai sun rinjayar da rashin aukuwar sakinsa ne, saboda faɗin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):_

لَا طَلَاقَ وَلَا عِتَاقَ فِي إِغْلَاقٍ
Babu saki ko ’yantawa a cikin rufewar hankali ko tilasci.
_Sahih Abi-Daawud: 1919_ .

Wannan kuwa mun ji da zaɓin-ransa ya sake ta a gaban mutane, ba tilasta masa aka yi ba!

[3] Abu na-uku: Ba a buƙatar sanin manufarsa a Saki Sarihi. Saki Sarihi shi ne wanda ake fahimtar ma’anar sakin a cikinsa, wanda kuma ba ya ɗaukar wata ma’ana ko fassara in ba sakin ba. Kamar mutumin da ya ce wa matarsa: Na sake ki! Ko kuma: *Ke sakakkiya ce!*

Malamai sun yarda cewa: Duk wanda ya gaya wa matarsa wannan irin furucin, to matar ta saku. Kuma ko da ya yi da’awar cewa ba sakin yake nufi ba, ba za a yarda da shi ba. _(Fiqhus-Sunnah: 3/17)._

[4] Abu na-huɗu: Saki uku, ɗaya ne daga cikin sakin bidi’a idan aka aukar da shi a lafazi guda ko kuma aka maimaita shi a mazaunin guda. Game da aukuwarsa kuwa malamai sun yi saɓani mai tsanani. Amma mafi kyau daga cikinsu shi ne cewa: Ya auku a matsayin saki guda ɗaya ne wanda ake iya yin kome a cikin iddarsa. Domin haka abin ya ke a zamanin Manzon Allaah _(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)_ da Abubakar da farkon zamanin Umar _(Radiyal Laahu Anhu)._

[5] Abu na-biyar: Lallai mu san cewa: Hukuncin Alƙali shi yake yanke dukkan rikici a tsakanin al’umma. Don haka, tun da uwar yarinyar tana da ra’ayin cewa saki uku uku ne, to ba yadda za a yi sai dai a ɗauki maganar zuwa gaban alƙalin musulunci, don ya yanke musu hukunci a ƙarƙashin *Al-Kitaab Was Sunnah Alaa Fahmi Salaf As-Saalih.*

_Wal Laahu A’lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
20/7/2019
6: 54am.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now