*ADALCI A TSAKANIN MATAYE WAJIBI NE!*

322 6 0
                                    

*028 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*ADALCI A TSAKANIN MATAYE WAJIBI NE!*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum warahamatullah. An tashi lafiya ya aiki? Dan Allah ina da tambaya, mutum ne ya ajiye mata uku, sai ya je gina dakuna ciki uku, sai ya gyara ma sauran amma ya ki gyara ma uwargidan, mene hukuncinsa?

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu wa rahmatullah. Lallai wannan ko shakka babu zalunci ne, ya kamata kamar yadda aka gyara wa kowa ɗakinta ita ma uwar gida a gyara mata nata dai-dai da dai-dai, rashin yin hakan zai iya sa a kira wannan miji da azzalumi a harkar jagorancin gidansa, daga cikin sharaɗin yin mata fiye da ɗaya, mutum ya tabbatar zai yi adalci a tsakanin matayensa, idan mutum yana tsoron ba zai iya yin adalci a tsakanin matansa ba, an ce ya tsaya a auren mata ɗaya kacal, kamar yadda aya ta uku (3) cikin suratun Nisá'i tabayyana.

Sannan kuma a wani wurin Allah maɗaukakin sarki ya ce:
"KADA KU YI ZATON ALLAH BAI SAN ABIN DA AZZALUMAI SUKE AIKATAWA NE BA...".
Suratu Ibrahim aya ta 42.

Manzon Allah s.a.w a wani hadisi cewa ya yi:
"DUK WANDA YAKE DA MATA BIYU, SAI YA KARKATA WAJEN GUDA XAYA, ZAI ZO A RANAR ALQIYAMA SASHEN JIKINSA A SHANYE".
Abu Dáwud ya ruwaito a hadisi mai lamba 2133.

Don haka mazaje masu yin irin wannan zalunci ga matayensu ana ji masu tsoron faɗawa cikin irin wannan mummunan hali, saboda Allah ba ya zalunci, kuma ya haramta a yi zalunci, don haka mu ji tsoron Allah mu yi adalci a tsakanin iyalanmu. Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
2/5/1440 h.
08/01/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now