AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

816 21 0
                                    

TAMBAYA 1,309
Assalamu'alaiku malam inaneman sanine akan addu'ar da'akeyi in anga watan ramadan? Dakuma addu'ar da'akeyi lokacin suhur? sannan da addu'ar da'akeyi lokacin budebaki? Dafatan Allah Yakara Wa Malam ilimi Amin.
AMSA
Babu wata addu'a da ta tabbata a sunna game da ganin watan ramadan a iya sanina sai dai idan anga jaririn wata kowanne annabi ya karantar damu addu'ar da akeyi wannan kuma bai keɓanci ramadan kaɗai ba, sannan ban san wata addu'a daga sunna ba a lokacin sahur bayan bismillah lokacin fara cin abinci, sannan a lokacin buɗe baki akwai addu'o'i masu yawa da annabi ya karantar da mu daga ciki akwai ((zahabazzama'u wabtallatul uruƙu wa sabatal ajri insha Allah)).
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

TAMBAYA 1,311
Assalamu Alaikum malam ya halatta mutum yayi kitson zare irin wanda ake barin space a tsakanin zare da zare(some gaps)?
AMSA
Shi gyran gashi abu ne mai kyau a musulunci saboda annabi (saw) yana gyara gashinsa ko matansa su gyra masa, sai a duba idan sa relaxer baya canja halittan Allah kuma ba ya sa ayi kamaceceniya da mata babu laifi don anyi, Sheikh uthaimin yace: Bai halatta mace tayi kitso da ulu (attachment) ko brazin ba ko koda kuwa miji ne yace yanaso matarshi tayi mishi ado dashi saboda jin tsoron kada ta zama cikin masu dashen gashi annabi kuma yace ((Allah ya tsinewa wanda akayi wa dashen gashi da wanda tayi dashen gashin)) annabi ya gaya mana cewa abinda mata suke sakawa akai wanda ba gashinsu ba kamar a cuci maza da ulu da brazin yasa Allah ya halakar da banu isra'il saboda mazansu suna kallo basu hana su ba don haka wannan aiki na janyowa al'umma fishin Allah da kuma har ma ya halakar da ita, gwanda mace ta tsaya da iya gashin da Allah ya azurtata dashi don yasan shine mafi dace wa da ita. Allah ya ganar da matanmu.
Wannan bayani na cikin linnisa'i fakaɗ shafi na 331
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now