*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*LAULAYIN CIKI NA SA NI YIN AMAI A SALLAH, YAYA HUKUNCIN SALLATA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Malam ina maka fatan alkairi dan Allah a amsa min wannan tambayar. Malam mace mai juna biyu tana fama da yawu, to ko da yaushe sai in da abin taunawa a bakinta, ko sallah za ta yi, in kuma ba ta sa abu a bakinta ba to za ta yi amai tana cikin yin sallar. To malam mene ne matsayin sallarta? nagode.
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu, Lallai cin abinci a cikin sallah yana ɓata sallah, kamar yadda duk malaman Fiqhu suka tabbatar, to amma shi ko amai ba ya ɓata sallah, saboda amai ba najasa ba ne, don haka bai halasta ta yi sallah tana tauna komai a bakinta ba, kawai ta yi sallarta a haka, ta sami kyallaye ko tsumma yalwatacce kuma mai tsafta da idan amai ɗin ya zo mata za ta yi a ciki, ta share bakinta, ta kuma ci gaba da yin sallarta, kuma sallarta ta inganta a hakan.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
25/6/1440 h.
02/03/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: