*SHARAƊI A CIKIN KASUWANCI

245 0 0
                                    

*TAMBAYA TA 021*

*SHARAƊI A CIKIN KASUWANCI*

_Assalamu Alaikum,_ da fatar malam yana cikin ƙoshin lafiya.

Mutum ne ya ba ni kuɗi in yi kasuwanci amma da sharaɗin duk wata ga abin da zan rinƙa ba shi. Shin malam wannan ba riba ba ce?

Allaah ya saka wa malam da Gidan Aljannar Fardausi. Ameen.

*AMSA A021*

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._

Allaah ya saka mana gaba ɗaya.

Malamai sun yarda cewa: Wani ya bayar da kuɗi, wani kuma ya riƙa yin kasuwanci, a ƙarshe kuma su riƙa raba ribar da aka samu da gwargwadon yadda suka yi sharaɗi tun farko a tsakaninsu daidai ne. Wannan ne suke kira: *Mudaarabah.*

Amma a irin wannan halin da ake tambaya a kansa, inda ba a san nawa ne ribar da aka samu ba, sai dai kawai duk wata mai kuɗi ya riƙa zuwa yana karɓar wani adadi da aka amince a kansa tun farko, ban san madogarinsa a shari’a ba.

Musamman ma da yake a cikinsa akwai cutarwa da takurawa ga mai gudanar da kasuwancin, domin ai bai san ko riba za a ci, ko kuwa faɗuwa za a yi a cinikin wannan watan ba. Idan kuma mai kuɗin ya cigaba da karɓar kuɗi duk wata, za a wayi gari kenan uwar kuɗin da aka fara kasuwancin ma da ita ta ƙare!

Zai kuma iya yiwuwa a riƙa samun riba mai yawa a cikin kasuwancin, ta yadda mai kasuwanci ne zai cigaba da samun fa’ida, shi kuma mai kuɗin zai riƙa cutuwa. A ƙarshe ya zo yana cizon yatsa.

Abin da ya fi dai kawai sai su zauna su sake tsarin don ya dace da koyarwar addini. Ko da ɗaya bisa goma (1/10) na ribar ce mai kuɗin zai riƙa karɓa ya bar wa mai kasuwancin tara bisa goma (9/10) ya fi daidai, _in sha’al Laah._

Ba za a ce wannan  riba ba ce. Abin da ya yi kusa da wannan a babin riba, shi ne abin da malaman Fiqhu suke kiransa: *Ribal Qard,* watau: Riba na bashi. Shi ne mutum ya bayar da bashin da a ƙarƙashinsa zai samu wani amfani, kamar yadda suke cewa:

*كل قرض جر نفعا فهو ربا*
*Duk wani bashi ko rancen da ya janyo amfani, to Riba ne.*

Sai dai kuma a fili ya ke cewa, wannan ba bashi ya bayar ba, yarjejeniyar ciniki ce ba a ajiye ta yadda ya dace ba.

_Wal Laahu A’lam._

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now