*AMSOSHIN *TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN WANDA HAILA TA ZO MATA DAI-DAI LOKACIN SHAN RUWA*
TAMBAYA:
Salamun aleikum malam, Allah gafarta malam da fatan an sha ruwa lafiya, don Allah malam ina da tambaya, tambayata ita ce shin malam ina azumi, na yi sallar azuhur da la'asar, ban yi magariba da lisha'i ba sai na ga al'ada ta zo min, shin abin da nake so na sani akwai azumina ko babu shi? Na gode.
Amma fa sai da na sha ruwa sannan na ga al'adar ta zo amma ban yi sallar magariba da lisha'i ba.AMSA:
Wa'alaikumus salam, ƴar uwa matuqar al'ada ba ta zo maki ba sai bayan da rana ta faɗa, ko da ba a yi sallar magriba ba, to azuminki na wannan yini ya inganta da ikon Allah, ba wata matsala da ta same shi, kasancewar ba ki yi sallar Magriba da Isha'i ba haila ta zo maki, wannan bai ɓata maki azuminki ba, saboda lokacin azumi yana farawa ne daga ketowar Alfijir zuwa faɗuwar rana, to ke kuma sai bayan da rana ta faɗa sannan hailar ta zo maki, ga shi ma har ruwa kin ce kin sha, saboda haka azuminki ya inganta, in da a ce kafin rana ta faɗa ne haila ta zo, to da sai a ce azumi ya ɓaci.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
7/Ramadan/1440 h.
12/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: