*WACCE IRIN RANTSUWA CE KE WAJABTA YIN KAFFARA?*

787 3 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*WACCE IRIN RANTSUWA CE KE WAJABTA YIN KAFFARA?*

TAMBAYA:

Assalamu Alaikum, don Allah ina so ayi min cikakken bayani akan irin rantsuwar da take wajabta kaffara, saboda an maida ta kamar al'ada cikin al'umma, wallahi kaza wallahi kaza, Meye cikakken bayaninta? ngd.

AMSA:

Wa'alaikumus Salamu, Ba kowace rantsuwa ce take wajabta yin kaffara ba, rantsuwar da take wajabta yin kaffara ita ce rantsuwar da aka yi ta da nufi, mutumin da ba a san shi da yawan rantse-rantse a maganganunsa ba, sai kawai yana cikin magana sai ya qarfafa maganarsa da yin rantsuwa da nufinsa har zuci, to matuqar bai aikata wannan abin da ya rantse a kansa ba, to kaffara ta wajaba a kansa. Ko kuma mutumin da zai rantse da cewa Wallahi ba a isa a yi abu kaza ba, sai kuma aka aika ta wannan abun, to shi ma wannan kaffara ta wajaba a kansa.

Kaffarar da ke kansa ita ce ciyar da miskinai goma, ko ɗinka masu tufafi, ko ƴanta kuyanga. Kamar yadda ayar Alqur'ani ta bayyana.
Suratul Ma'ida 89.

Amma idan mutum mai yawan rantse-rantse ne a zantuttukansa, ta zama masa al'ada a cikin maganganunsa na yau da kullum, duk wata magana da zai yi sai ya haɗa ta da rantsuwa, kamar mutum ya ce: "wallahi yanzu na dawo, wallahi da muka je garin su wane, ba zan sha ba wallahi, wallahi kai dai a yi sha'ani kurum",  irin wannan rantsuwa ita ce ake kira YAMINUL LAG'WI, mai yin wannan ya mayar da ita al'ada a maganganunsa, to Allah ba ya kama bayinsa da irin wannan rantsuwa, wato ba ta wajabta yin kaffara, kamar yadda Allah S.W.T ya bayyana a farkon aya ta 89 da ke suratul Ma'ida.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
26/6/1440 h.
03/03/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now