*MATAR AURE MAI HIRA DA TSOFAFFIN SAMARINTA*

141 3 0
                                    

*TAMBAYA TA 126*

*MATAR AURE MAI HIRA DA TSOFAFFIN SAMARINTA*

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,

Na tsinci memory-card ne a gidanmu, sai na sa a wayata don in gano wanene mai shi. Sai kuwa na gano na kishiyar mamata ne, kuma a ciki sai na ji ta adana hira da ta yi da tsofaffin samarinta, tana yin maganar batsa da kalmomi marasa daɗi da su. To, shin in sanar da mahaifinmu ne, ko in yi mata nasiha kawai? Wace shawara dai za a ba ni a nan?

AMSA A126:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

(i) Tun da farko bai kamata ka/ki sanya memory-card ɗin a cikin wayarka/ki ba, matuƙar dai ka/kina iya gano mai shi ta wata hanyar ta daban, kamar ta hanyar cigiya da sanarwa a cikin gidan don neman wanda ya yar da sim-card ɗinsa mai alama ko launi kaza da kaza.

(ii) Idan kuma ya zama dole sai ta wannan hanyar ce kawai za ki iya gano mai shi, to za ki yi hakan ne da gwargwadon buƙata kawai, amma ba tare da kutsawa a cikin abin da ya shafi sirrin mai memory-card ɗin ba.

(iii) Bai halatta ki sanar da mahaifinka/ki ko wani daban, kamar mamanka/ki a kan wannan abin ba, domin kar ka/ki zama sanadin aukar da fitina a tsakanin ma’aurata. Sai dai ko in akwai wata hujja ƙwaƙƙwara ce cewa barin hakan zai kai ga aukuwar wata cuta gare shi, ko ga sauran iyalin gidan idan ka/kika ɓoye abin.

(iv) Abin da ya wajaba gare ka/ki shi ne ka/ki mayar mata da  ɗin kawai, baki-alaikum. Idan kuma memory-card iya yi mata nasiha don ta ji tsoron Allaah, ta kiyaye girmanta da matsayinta, ta daina ajiye irin wannan hirar a cikin wayarta, to wannan ma daidai ne.

Wal Laahu A’lam.

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
26/8/2019
11: 11pm

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now