*ZAN IYA CIN BASHIN BANKI SABODA ZUWA HAJJI ??*
*Tambaya*
Assalamu alaikum, malam don Allah ina da tambaya kamar haka - ko zan iya cin bashin banki wato loan domin cika kudin kujerar maka,? Nabiya ma mahaifiyata sabida karin kudin da akayi ya wuce abinda muke zaton cikawa kuma ni ma'aikaciyar gwamnati ce. Na gode Allah yabada ikon amsawa.
*Amsa*
Wa alaikum assalam,
mutukar ba ki da hali to barin zuwa aikin hajjin shi ne daidai,, saboda Allah ya kwashewa kudin ruwa albarka a cikin suratul Bakara kuma ya yi shirin fito-na-fiton yaƙi da wanda ya ci riba,, sannan Allah bai wajabta miki hajji ba ta hanyar bashi,, balle kuma ki biyawa wani.Hajji yana wajaba ne ga wanda yake da iko da kuma isasheshen guzirin da zai wadatar da shi daga rokon mutane.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR.JAMILU YUSUF ZAREWA*
*5/6/2017*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Cerita Pendek*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: