*027 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN SALLAR RAWATIB NA KAFIN AZUHUR YANA INGANTA A LOKACIN WALHA?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahmatullah. Malam sallolin da ake yi a rana masu raka'a sha biyu na rawatib, biyu kafin sallar Asuba, hudu kafin sallar Zuhur, biyu bayan sallar Zuhur, biyu bayan sallar Magrib, biyu bayan sallar Isha'i, to malam abin da ban fahimta ba a nan shi ne, hudu kafin sallar Zuhur zan iya yin su a lokacin sallar Duha (Walha) ko sai lokacin da zan yi sallar Zuhur zan yi su, sannan in na gama in yi sallar Zuhur din? Nagode mallam Allah yakara basira amin.
AMSA:
Wa'alaikumus Salamu Wa rahmatullah. Sallolin sunnar Rawaatib suna da lokutan yin su kamar yadda ya tabbata daga Manzon Allah s.a.w a Bukhariy da Muslim, haka nan ita ma sallar Walha tana da nata lokacin kamar yadda shi ma hadisin da Muslim ya ruwaito ya tabbatar, saboda haka kowanne za a yi shi ne a lokacinsa, ba za a shigar da wani cikin lokacin wani ba. Wato kenan ba za a yi raka'o'in rawatib huɗun nan a lokacin Walha ba, za a bari ne sai Rana ta yi zawali lokacin Azuhur ya shiga sannan a yi raka'o'in Sallar Rawatib na kafin Azuhur.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
1/5/1440 h.
07/01/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: