AMSOSHIN TAMBAYOYINKU

431 9 0
                                    

*TAMBAYA TA 090*

*SADAKA DA KAYAN KIRISTA*

_As-Salamu Alaikum,_

Tambaya ce da ni: Na sayi kaya ne daga wurin wata Kirista, da na koma gida sai na ga ta yi min ƙari a kai. Na yi ta komawa wurin ina neman ta, daga baya sai aka fada mini cewa: Yanzu ta daina kawo kaya wurin. Ban san ta ba, kuma ban san inda zan same ta ba, to zan iya yi mata sadaka da kayan da ta ƙara mini?

*AMSA A090*

_Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah._

[1] Da farko ina roƙon Allaah ya yi miki albarka, kuma ya ƙara tsare ki kuma ya ƙara daidaita ki, kuma ya kafe ki a kan hanyar alheri, ta nisantar cin haram har zuwa mutuwarki. A irin wannan lokacin da yawancin mutane – in ban da waɗanda Allaah Ubangijin Halittu ta tsare su ba – suka mayar da cin haram ba komai ba ne, aka samu mai neman kaucewa da tsare kai daga abin da bai halatta ba! Wannan babban abin yabawa ne. Don haka ina ƙara yaba miki, da roƙon Allaah ya yawaita masu irin wannan halin a cikin al’umma.

[2] Abu ne sananne a cikin Addinin Musulunci cewa: Wajibi ne a kan musulmi ya tsare wa jama’a haƙƙoƙinsu. Bai halatta ba, kuma ma haram ne a fili ƙarara musulmi ya ci haƙƙoƙin da ba nasa ba, ko da kuwa waɗannan haƙƙoƙin na kafiran da ba musulmi ba ne, waɗanda suke zama a cikin musulmin. A cikin _Surah Al-Mumtahinah: 8,_ Allaah ya ce:

لا ينهاكم الله عن الذين لم يقاتلوكم في الدين ، ولم يخرجوكم من دياركم أن تبروهم و تقسطوا إليهم ، إن الله يحب المقسطين
Allaah ba ya hana ku ba dangane da waɗannan (kafiran) da ba su yaƙe ku a cikin Addini ba, kuma ba su fitar da ku daga cikin gidajenku ba, cewa: Ku yi musu alheri kuma ku yi musu
adalci. Haƙiƙa! Allaah yana son masu adalci.

Sannan kowa ya san cewa: Duk lokacin da ya ci haƙƙin da ba nasa ba, kome ƙanƙantarsa kuwa, to lallai zai zo da shi a ranar Al-Qiyama. Kuma ba zai shiga Aljannah ba sai daga bayan ya gama biya masu haƙƙoƙinsu. Allaah ya kyauta. Allaah ya tsare mu.

[3] Amma game da haƙƙin wannan mace Kirista da ke hannunki, ina ga hanyoyin da za ki bi don isar da shi gare ta suna da yawa, kuma ba a gama ba balle a yi maganar yi mata sadaka da shi.

(i) Da farko, ki yi ƙoƙarin tambayar abokan zamanta a kasuwa, waɗanda suke zama tare da ita ko a kusa da ita.

(ii) Ko kuma masu sayar da irin kayanta daga cikin masu yarenta da addininta.

(iii) Sai kuma masu jin yarenta mabiya addininta ko da ba su sayar da irin kayan sayarwarta.

(iv) Sannan ko kuma waɗanda ba yarenta ba, ba addininta ba.

(v) ko kuma ta hanyar sarkin kasuwa.
Me yiwuwa a dace wani ya gane ta, kuma ya zama zai iya yin magana da ita. Sai ya sanar da ita cewa akwai haƙƙinta a kanki wanda kike so ki mayar mata.

[4] Idan ba a iya samun biyan bukata ta waccan hanyar ba: Ba a samu wanda ya san ta, ko zai iya haɗuwa ko yin magana da ita ba, sai ki sauya hanya:

(i) Ki yi ƙoƙarin samun lambar wayarta daga maƙwabtanta a kasuwa ko mutanen addininta ko yarenta ko masu sayar da irin kayanta.

(ii) Ko kuma ki bi ta hanyar wasu shugabannin addininta, kamar waɗanda suke zama don tattaunawa da malaman musulmi.

(iii) Ko ki bi ta hanyar jami’an tsaro, kamar ’yan sanda ko Civilian JTF ko jarumai da gora, wataƙila wani daga cikinsu ya san wani daga cikin mutanenta.

Me yiwuwa a samu dacewa, wani ya isar da saƙon a cikin jama’an yankinsu, har ita kuma ta ji.

[5] Idan ba a samu biyan buƙata ta wannan hanyar ba sai a sauya wata:

(i) Sai ki tafi Filin Cigiya da Sanarwa na Gidan rediyo/tv, ki sanar da su lokaci da wurin da abin ya auku.

(ii) Ki bayyana musu nau’in da yanayin kayan da bayanin adadi ko girman kayan, da yadda aka yi har ya zo hannunki, yanzu kuma kike son mayar mata. Me yiwuwa a dace ta hanyarsu.

Za ki ɗauki waɗannan matakai ne idan kayan masu daɗewa a ajiye ne ba masu saurin lalacewa ba, kamar tufafi ko takalma ko jakunkuna ko littaffai, ko kayan abinci kamar masara gero da dawa da sauransu.

Amma idan abubuwa ne waɗanda ba za su ajiyu ba, kamar kayan miya irin su tumatir tattasai da kuɓewa da sauransu, za ki iya yin amfani da su, kuma ki ɗauki waɗancan matakan na nemanta. Idan an same ta sai ki biya ta kuɗin kayan, bayan kin bayyana mata.

Idan kin bi irin waɗannan hanyoyin kuma ba a samu biyan buƙata ba, a nan kya iya yin sadaka da kayan, amma a duk ranar da kuka sake ganinta sai ki biya ta.

Ɗaukar waɗannan matakan akwai wahala a yau, amma kuma tabbas sun fi sauƙi ga mai Imani da tsoron Allaah fiye da matsalar da za ta iya taso wa idan aka haɗu da mai kayan a gaban Allaah Ubangijin Halittu a Ranar Lahira.

Domin gudun aukuwar irin wannan matsalar ya kamata mu riƙa tsayawa muna lura da kyau a lokacin sayayya da mutane, mu yi ƙoƙarin saninsu sosai kafin rabuwa.

Allaah ya taimake mu, ya sa mu iya sauke dukkan haƙƙoƙin jama’a da suke kanmu kafin rasuwarmu.

_Wal Laahu A’lam._
_5/5/2019_
_10: 08am._

*sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now