*AZUMIN NAFILA RANAR ASABAR !*
*Tambaya*
Assalamu alaikum
Dr. maganar azumi wani malami yace : indai kamata ne mutum yayi Alhamis da Juma'a, don anyi hani da yin azumi ran sati ?*Amsa*
Wa'alaikumus salam
To 'yar'uwa hadisi ya zo daga Annabi s.a.w cewa : "Kada ku yi azumi ranar asabar sai abin da aka farlanta muku" Abu-dawud hadisi mai lamba ta :2423.
Saidai malamai sun yi sabani akan ingancin wannan hadisin, akwai malaman da suka tafi akan cewa hadisin karya ne, Abu-dawud ya hakaito hakan daga Imamu Malik.Akwai wadanda suka inganta shi, akwai kuma malaman da suka ce hadisin akwai kuskure a ciki, saboda ya sabawa hadisin da ya fi shi inganci, inda Annabi yake cewa : "kada dayanku ya azumci ranar juma'a, sai in ya azumci yinin da yake gabaninta, ko kuma wanda yake bayanta" Bukhari a hadisi mai lamba ta : 1884, wannan hadisin yana nuna halaccin azumtar asabar ga wanda ya azumci juma'a.
Akwai malaman da suka tafi akan cewa wannan hadisin an goge shi da wasu hadisan, saboda yadda aka rawaito cewa annabi yana azumtar mafi yawan Sha'aban, wannan sai ya nuna cewa dole asabar ta fado a cikin azuminsa, ga shi kuma Annabi s.a.w. ya halatta irin azumin Annabi Dawud, wanda za ka yi azumi yau ka sha gobe, babu yadda za'a yi mutum ya yi azumin Annabi Dawud ba tare da Asabar ta fado a cikin azubinsa ba.
Zancen miliyoyin malamai shi ne ya halatta ayi azumi ranar asabar ga wanda ya yi azumi ranar juma'a.Don neman karin bayani duba: Tahzibu sunani Abidawud 1\469
Allah ne mafi sani
*_Dr. Jamilu Zarewa_*
23\10\2015
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: