*YADDA AKE YIN SALLAR ISTIKHARA

1.6K 2 0
                                    

*010 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YADDA AKE YIN SALLAR ISTIKHARA*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum malam. Dan Allah ina son a yi min bayanin yanda ake Sallar istihara. Allah ya qara ilmi mai amfani.

AMSA:

Wa'alaikumus salam. Sallar istikhara sallah ce da ake yin raka'o'i guda biyu kamar yadda ake yin sauran sallolin nafila, abin da ke bambanta su shi ne niyya, ana yin sallar istihara ce don barin ma Allah zaɓi a kan wata buqata da mutum ke da ita. Sannan kuma Sallar istikhara sunnah ce ba farilla ba. Bayan mutum ya kammala sallar, sai ya karanta wannan addu'ar:

اللَّهُمَّ إنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ , وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ , وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِرُ , وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَمُ , وَأَنْتَ عَلامُ الْغُيُوبِ , اللَّهُمَّ إنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ (هنا تسمي حاجتك ) خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي أَوْ قَالَ : عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ , فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ , اللَّهُمَّ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ (هنا تسمي حاجتك ) شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي أَوْ قَالَ : عَاجِلِ أَمْرِي وَآجِلِهِ , فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ ارْضِنِي بِهِ . وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ.

MA'ANA:

Ya Allah ina ba ka zaɓi da iliminka, ina neman iyawa daga ikonka, ina nema daga falalarka mai girma, domin kai kake iyawa, ni ba na iyawa, kai ne kake da sani, ni ba ni da sani, kuma kai ne masanin gaibubbuka (gaibu), ya Allah in dai a iliminka wannan al'amari (A NAN SAI MUTUM YA AMBACI BUQATARSA) sharri ne a gare ni a addinina da rayuwata, da mokomar al'amarina, ka juyar da shi daga gare ni, ka kuma juyar da ni daga gare shi, ka qaddaro mini alhairai a duk inda yake, sannan ka yardar mini da wannan abu (A NAN MA ZAI AMBACI BUQATARSA). Bukhari ya ruwaito a hadisi mai lamba 1166.

Ana karanta addu'ar ce bayan an idar da sallar an yi sallama, sai mutum ya ɗaga hannuwansa sama, ya yi yabo da jinjina ga Ubangiji, sannan ya yi salati ga Annabi Muhammad s.a.w. daga nan kuma sai ya yi ita waccan addu'ar ta istikhara, bayan ya gama sai ya sauke hannayensa kawai ba sai ya shafa a fuska ba.

Kuma ya halasta ga wanda ba ya iya yin ta da Larabci ya furta ma'anoninta da Hausa, ko kuma da duk harshen da yake iyawa, amma a yi addu'a da Larabci shi ne aula kamar yadda malaman Fiqhu suka bayyanar.

Wannan shi ne yadda ake yin sallah da addu'ar Istikhara, kuma kai ake so ka yi da kanka, ba wani ne zai yi maka ba, wannan ita ce Sunnah.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria*
5/4/1440 H.
12/12/2018 M.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now