*031 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*SHIN SALLAR ISTIKHARA TANA DA LOKACI NE KEBABBE?*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum malam. Dan Allah ina da tambaya? Idan ana sallar istikhara sai mutum ya kai Juma'ah 3 yana yi, sai Juma'ah ta hudu bacci ya yi mai nauyi sosai bai tashi ba sai 4:30. A lokachin zai iya yin ta?
Shin Idan bai yi ba a wannan ranar zai dawo baya da qirgen sati ne?
Allah ya qara sani mai amfani ameen. Na gode malam.AMSA:
Wa'alaikumus Salamu wa Rahmatullah. Hmhmh, ƴar uwa ai kin ba kan ki aiki ne kawai, ita Salatul Istikhara ba a ce dole sai ranar Juma'a a ke yi ba, sannan ba a ce sai mutum ya yi ta yi har zuwa wani adadi qididdigagge ba, sannan ba a ce sai mutum ya tashi a cikin dare sannan zai yi ta ba.
Saboda haka, kodayaushe kina iya yin sallar istikhara matuqar ba a lokutan da aka karhanta yin sallah ba ne, kamar bayan sallar La'asar, da bayan sallar Asuba, waɗannan lokuta an qyamaci yin sallah a cikinsu.Za ki iya yin sallar Istikhara a duk ranar da kika buqaci yi, kuma a duk lokacin da kika samu dama, matuqar ba a lokutan da aka hana yin sallah a cikinsu ba ne.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
8/5/1440 h.
14/01/2019 m.

YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: