*YA MATSAYIN HADA ABINCIN DAN AIKIN GIDA DA NA CIYARWAR SHAN AZUMI?*

157 3 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA MATSAYIN HADA ABINCIN DAN AIKIN GIDA DA NA CIYARWAR SHAN AZUMI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, ciyar da miskini da me azumi zai yi, idan mutum yana da almajiri, shin zai iya hada mishi abincin mutum biyu waje daya, idan yaje makarantan su yaba wani almajirin rabi, kasancewar ana mishi kwanu uku, da na kunu, da na abin da aka soya, sai kwanon abinci kuma, don Allah a taimaka min da wannan tambayan.

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, Haqqin ciyar da miskini ga wanda ya sha azumi saboda lallurar da ta sa aka ba da damar ciyarwar, da kuma haqqin abincin almajirin gida mai yin maku aiki, waɗannan haqqoqi ne guda biyu mabambanta, kowanne yana zaman kasansa ne, saboda haka bai dace a haɗa abincin almajiri mai aikin gida da kuma abincin ciyarwar azumin da aka sha saboda lallurar da ta ba da damar yin haka ba

A yi ma kowa kwanonsa daban, sai a sanar da shi almajirin cewa su riqa zuwa tare da waninsa su karɓa tare, saboda a kauce wa faɗawa cikin shubha.

Allah ne masani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
23/Ramadan/1440 h.
28/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now