*YA HUKUNCIN DIBAR KUDIN ATTAJIRIN MIJIN DA BA YA WA MATARSA KYAUTA BAYAN HAQQI

95 0 0
                                    

*204 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN DIBAR KUDIN ATTAJIRIN MIJIN DA BA YA WA MATARSA KYAUTA BAYAN HAQQI NA WAJIBI?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, malam da fatan an wuni lafiya, dan ALLAH ina da tambaya, tambayata ita ce misali kana da miji mai kudin gaske. Amma ya tsare maka ci da sha da sutura amma ba ya daukar kudi ya ba ka sai ya yi shekara daya bai ba ka kyautar ko kwandala ba, ko da kudin recharge card. To mallam in ya ajiye kudinsa ka dauka a boye ba tare da ya sani ba kana da laifi?

AMSA:

Wa'alaikumus salam, ƴar uwa magana ta gaskiya ita ce wacce muka faɗa a Amsoshin Tambayoyinku na 192, wato matuqar miji yana kiyaye haqqoqin ciyarwa na wajibi ga iyalansa, to bai halasta su ɗebi kuɗinsa su yi amfani da shi da sunan ba ya masu kyauta ba, dama ita yin kyautar bayan an ba da haqqi na wajibi ba dole ba ne. Duk matar da ta sake ta ɗibi kuɗin mijinta ba tare da saninsa ba saboda ba ya mata kyauta, ko saboda ba ya siya mata recharge card, to ta sani tabbas haramun ta ɗiba, kuma ta yi zamba cikin aminci, za ta biya shi a ranar gobe Alqiyama.

Inda kawai shari'a ta ɗaga qafa wurin ɗibar kuɗin miji a yi amfani da su ba da saninsa ba, shi ne inda aka yi rashin sa'a miji ya zama maqeqe, ga kuɗin amma ba ya isa wurin haqqin ciyarwa na wajibi kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: (5364) ya bayyana.

Allah S.W.T ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
7/12/1440 h.
08/08/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now