*205 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN HALARTAR SALLAR EIDI GA MAI TAKABA*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Don Allah malam ya hallata mai TAKABA ta je sallar idi? Na gode Allah ya qara wa malam lafiya.
AMSA:
Wa'alaikumus salam, Matar da mijinta ya rasu wajibi ne ta yi idda (takaba) na wata huɗu da kwana goma kamar yadda aya ta 234 na suratul Baqara ta tabbatar. Idan kuma mai ciki ce mijinta ya rasu, iddarta za ta kasance har zuwa lokacin da za ta haifo wannan ciki ne.
Ya wajaba a kanta ta zauna a gidanta a lokacin iddar, ba za ta fita ba sai da uzuri na Shari'a, ko wata buqata ta tilas, daga cikin uzurori na Shari'a su ne kamar zuwa asibiti neman magani, ko zuwa wurin alqali idan ya buqaci hakan saboda tattara bayanan dukiyar gado, ko wasu daga cikin uzurori da suka tilasta mata fita, amma idan ba wani sababi, to ba ya halasta ta fita daga gida, a bisa wannan bayani sai ya zama ba ya halasta a gare ta ta fita ziyara zuwa wurin maqwabtanta, ko ƴan uwanta, ko halartar sallar Eidi, ko abin da ya yi kama da haka, za ta zauna a gida ne har ta kammala takabar... Kamar yadda Sheikh Ibn Uthaimeen ya bayyana.
Dubi Fataáwá Nurun Alad Darb 19/2.Imamu Malik a cikin Muwaɗɗa ya ruwaito cewa Sayyiduna Umar ɗan Khaɗɗab Allah ya qara masa yarda ya kasance yana hana waɗanda mazajensu suka rasu zuwa aikin Hajji. Muwaɗɗa 2/591.
Wato wannan sai ya nuna tsananin yadda Shari'a ta buqaci mace mai takaba ta zauna a ɗakinta ba tare da zuwa ko'ina ba. Saboda haka mace mai takaba ba ta damar fita zuwa sallar Eidi, fitar da take da damar yi shi ne fitar da ta zama saboda uzuri ne karɓaɓɓe a Shari'a. Kawai ta zauna a ɗakinta ta yi ta maimaita kabbarbarin da ake yi a wannan lokaci, kamar: ALLÁHU AKBÁR, ALLÁHU AKBÁR, LÁ'ILÁHA ILLALLAH, ALLÁHU AKBÁR, ALLÁHU AKBÁR WA LILLÁHIL HAMDU.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
9/12/1440 h.
10/08/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: