*194 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN KWASHE WA MAGE ƳAƳANTA KAFIN TA YAYE SU*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu.
Malam mene hukunci a kan wadanda ke kiwon mage idan ta haihu 'ya'yan nata suka girma suka fara cin abinci sai su bayar da su ga wadanda suka nuna suna so, amma mahaifiyarsu ba ta yaye su ba sai dai in suka zo shan nono tana hantarar su kasancewar sun fara girma ba koyaushe take barin su su sha nonon ba. Amma idan aka bayar da su, bayan ta je tayo kiwo da daddare za mu yi ta jin kukanta tana kiran su su zo su ci abin da ta samo musu. Shin ana daukar alhakinta? Ngd.AMSA:
Wa'alaikumus salam, Tabbas ana ɗaukar alhakinta, ba ma ita kaɗai ba har ƴaƴan nata ma ana ɗaukar alhakinsu. Ba dai-dai ba ne a raba uwa da ƴaƴanta kafin yaye, yin hakan cutarwa ne, kuma Shari'a ba ta yarda a cutar da abin da bai cancanci cutarwa ba. A daina raba ta da ƴaƴanta har sai an tabbatar ta kammala yaye su, wannan ita ce maganar gaskiya.
Allah S.W.T ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
1/12/1440 h.
02/08/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: