ZAMA DA MIJI MAROWACI*

232 0 0
                                    

Tambaya ta 116

*ZAMA DA MIJI MAROWACI*

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah,
Mijin da yake sayo kayan sha’awa kamar nama da ’ya’yan itatuwa da kindirmo, wani lokaci ma har kaza yakan sayo, ya ce a sanya a miya, amma a tsame masa, ya ci shi kaɗai kawai, ko ’ya’yansa ba zai ba su ba, balle ma matansa! Lokacin da ɗaya daga cikin matansa ta ƙi yarda da hakan, sai ya daina yi mata magana, kuma ya daina sayo wa a ranar girkinta. To, don Allaah ina hukuncin shi mijin da ita matar? Kuma wace shawara za a ba ta dangane da zama da shi?

AMSA A116:

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Mun daɗe da amsa makamanciyar wannan tambayar. A nan ga kwafen tambayar da amsarta, tare da ’yan sauye-sauye:

TAMBAYA TA 033:
KO ZA TA IYA RABUWA DA MIJI ƘANƘAMO?
Assalamu Alaikum
Tambaya a kan miji irin ƙanƙamon nan, suna da arziƙi amma iyalansu ba su mora, iyakan abin da aka ce wajibi ne kawai yake yi mata, amma ban da sauran hidimomin rayuwa, sai dai iyayenta su yi mata. Ga rashin haƙuri, ga yawan kushe iyali, komai sai ya ce ba ta iya ba!
Menene shawara a nan? Domin matar ta fara ƙosawa da shi. Ya halatta ta rabu da shi, ta auri wani, ko za ta samu canjin rayuwa?

AMSA A033
W Alkm Slm W Rhmtul Laah.
Da farko, malama ai maganar ba ta kai ta rabuwa ba! Haƙuri za ki cigaba da yi da yawaita addu’o’in neman shiriya gare shi. Ko ba komai, ai ba ki san yadda mijin na-biyu zai kasance ba, ko da kin same shi. Kuma idan ba ki yi haƙuri ba, yaya za ki yi da ’ya’yanki, in akwai su? Wa za ki bari ya kula miki da su?
Abin da ya zama wajibi a kansa dai a nan shi ne, ya san cewa: Daga cikin mafi girman haƙƙoƙin matarsa a kansa akwai abin da Allaah Mabuwayi Mai Girma ya faɗa:
وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُفِ
Kuma ku rayu da su a cikin alheri

Kuma abu ne sananne cewa: Kyakkyawar rayuwa mai alheri ga mace ba ta tsaya ga ba ta tuwo da miya da rigar sallah da kuɗin zuwa awon-ciki a asibiti ba ne kaɗai, tana buƙatar sauran abubuwa domin ta kammalu, kuma ta kamantu da sauran mata matuƙar dai mijin yana da hali da iko.

Don haka, miji ba zai zama na-gari mai yawan alheri, kuma abin yabo da ƙauna a wurin Allaah da Manzonsa da sauran mutanen kirki ba, sai ya zama kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa:

خَيْرُكُمْ خَيْرُكُمْ لأَهْلِهِ ، وَأَنَا خَيْرُكُمْ لِأَهْلِي
Mafi-alherinku shi ne mafi-alherinku ga iyalinsa, kuma na fi ku alheri ga iyalina.

Kowa kuwa ya san cewa, ba shi daga cikin alheri mutum ya zama marowaci, ƙanƙamo mai baƙar rowa ga matarsa da iyalinsa, wanda yake bari har sai ita kanta ko iyayenta ne za su riƙa biya mata buƙatunta! Kamar yadda ba shi daga cikin alheri miji ya zama mai rashin juriya, mai yawaita suka da kushe matarsa ko iyayenta.

Kodayake ana cewa yawancin mata ba su da godiyar Allaah, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya nuna:

لَوْ أَحْسَنْتَ إِلَى إِحْدَاهُنَّ الدَّهْرَ ، ثُمَّ رَأَتْ مِنْكَ شَيْئًا قَالَتْ : مَا رَأَيْتُ مِنْكَ خَيْرًا قَط
Ko da ka kyautata wa ɗayarsu na tsawon zamani, daga baya kuma in ta ga wani abin ƙi a wurinka, sai ka ji ta ce: Ban taɓa ganin wani alheri ba a wurinka!

Amma dai duk da haka mutumin kirki ba ya bari a samu masoka gare shi a cikin zamantakewarsa da iyalinsa.
Bayan wannan, shawara a gare ki ita ce: Ki yi haƙuri, kuma ki riƙa tauna magana, ki riƙa bin abubuwa sannu a hankali kuma a cikin hikima. Ki yawaita yin addu’a ga Allaah ya sanyaya zuciyar mijinki, ya gyara halin shi, har ya san haƙƙoƙin da suka hau kansa dangane da Ubangijinsa da Manzonsa da Iyalinsa, kuma ya yi ƙoƙarin saukewa. Yawanci, nuna isa da gadara ba su sanya wa a samu biyan buƙata a wurin wasu mazan.
Amma idan abu ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa, to babu laifi ki sanar da magabatansa da farko kafin magabatanki, domin neman mafita.

Allaah ya shiryar da mu.

Wal Laahu A’lam.
27 – 03 - 2018

Allaah ya datar da mu ga dukkan alheri, ya kare mu daga dukkan sharri.

Wal Laahu A’lam.

*Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy*
29/7/2019
12: 04pm.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now