*_MATA TAGARI ABOKIYAR ZAMA A ALJANNA_*
Daga cikin siffofin mace ta gari akwai
*_Mace ta gari itace mai yin fishi idan mijinta yana fishi,mai yin dariya idan mijinta yana dari mai kuka da kukan mijinta_*wata rana Abdullahi bn Rawaha R.A ya fashe da kuka,sai matarsa itama ta fashe da kuka,sai ta tambayeta cewa:-
*_Mi ya sanya ki kuka_*,sai tace kukanka shine ya sanya ni kuka,sai yace da ita:
*_Ni ina kuka ne akan Na karanta acikin alqurani cewa zan bi ta kan wutar jahannama ,amma ba sani ba ko zan wuce ko bazan wuce ba_*
@سير اعلام النبلاء للذهبي - (236/1)]Daga cikin siffofin mace ta gari akwai:
*Tana kishi ga mijinta har bayan mutuwarsa kuma tana bin umarninsa har bayan mutuwarsa*.Daga Umma Dardaah matar Abud Dardaah R.A tana cewa:-
*_Kai ka nemi aurena a awajen mahaifana anan duniya,sai suka baka aurena ka aureni,to ni kuma ina neman auranka a Lahira_* sai yace:
*_To dan haka kada kiyi aure bayan mutuwa ta_* bayan ya rasu sai MU'AWIYYA R.A ya nemi aurenta sai taqi aurensa dan ta zauna da mijin a aljanna.
@الاصابة في تمييز الصحابة لابن حجر - (78/8)]Daga cikin siffofin mace ta gari akwai:
*Tana taimakawa mijinta acikin yin biyayya da dha'a ga Allah*.matar Habibul Ajamy ta kasance tana tada shi cikin dare dan yayi ibada sai tace:
*(Ka tashi ya mai gidana hakika dare ya tafi sosai,hakika lokacin bautar Allah na dare yana da riba mai yawa............)*.
@صفة الصفوة لابن الجوزي - (35/4)]Allah ne mafi sani
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: