YA HUKUNCIN RUWAN DA KE ZUBO WA MACE MAI KAMA DA MAJINA?*

142 8 0
                                    

*004 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YA HUKUNCIN RUWAN DA KE ZUBO WA MACE MAI KAMA DA MAJINA?*

TAMBAYA:

Assalamu alaikum, mallam tambayata ita ce mine ne hukuncin ruwan da ke fitowa a gaban mace mai kama da majina? Shin ko da tana alwala ya fito mata za ta iya sallah ba tare da ta sake alwala ba?

AMSA:

Wa’alaikumus salamu, wannan ruwa mai kama da majina da ke fita a gaban mace, idan har ya fito ba abin da za ta yi sai dai kawai ta yi tsarki, wato ta wanke wurin, sannan sai ta yi alwala.

Idan kuma tana cikin yin alwala ne ya fito, to ba za ta ci gaba da yin alwalan ba, za ta yanke ne, ta yi tsarki sannan ta qara sabunta alwalar.

Amma idan ya zama tasalsuli yake yi mata, wato yana fita akai-akai, to zai zama duk in za ta yi sallah sai ta yi tsarki sannan ta yi alwala, ko da tana cikin alwala ya zo mata ba za ta yanke ba, ya zamo mata lallura kenan.
Hukuncinta ya zama ɗaya da mai tasalsulin fitsari.

Allah ne masani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
01/12/2018

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now