*INA YIN WHATSAPP BA DA YARDAR MIJINA BA, YA HUKUNCINA

113 4 1
                                    

*021 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*INA YIN WHATSAPP BA DA YARDAR MIJINA BA, YA HUKUNCINA?*

TAMBAYA:

Don Allah malam mene hukuncin wanda mijinta ya saya mata waya, kuma ya ce kada ta yi WhatsApp, ita kuma sai ta yi, amma daga 'yan uwanta da take gaisawa da su, sai tambayah a kan abin da ba ta sani ba take yi, don Allah mene hukunci yin haka?

AMSA:

A gaskiya yin hakan da ta yi ba daidai ba ne, domin wannan saɓa wa umurnin miji ne, kuma saɓawa umurnin miji ga mata kuskure ne babba matuqar umurnin da mijin ya yi mata ba na saɓon Allah ba ne, kuma Allah zai tambaye ta a game da hakan, saboda ai shi yin WatsApp ba dole ba ne, kuma yin tambaya don a warware abin da ya shige duhu game da addini ba dole sai ta WatssAp ba, asali ai makaranta ce wajen neman ilimi ba ta Internet ba, musamman ma na addini saboda kaucewa gurɓatattun malamai da muggan aqidoji na ɓata, samun ilimi da fatawowi a gaban malamai shi ne aula, kuma shi ne asali, don haka ta daina yin WatssAp ɗin nan har sai ta sami yarda daga wajen mijinta, hakan shi ne mafi alheri a gare ta. Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki Zaria.*
20/4/1440 h.
27/12/2018 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now