*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN SA MAN-KADE A HANCIN MAI AZUMI SABODA MURA*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum.
Allah ya kara ma Malam lafiya. Tambayata ita ce Malam ni ne nake mura kuma na dauki azumi, to dan Allah zan iya sa mankade a cikin hancina?AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Duk magungunan da ake sa wa a hanci ko a ido, ko a kunni, mai azumi zai iya yin amfani da su don neman lafiya, saboda ba su daga cikin abin da ake kira ci ko sha, ko abubuwan da suke ɗaukan ma'anar ci ko sha, domin ci da sha ne aka hana, ba a shigar da abin da ba ya ɗaukar ma'anarsu a cikinsu, wannan shi ne zaɓin Shaikhul Islam Ibn Taimiyya, inji Allama Ibn Uthaimeen.
Amma idan da mutum zai sa maganin a hancinsa da nufin ya shiga cikinsa, to azuminsa ya karye.
Dubi Majmú'u Fataáwá 19/205 na Shaikh Ibn Uthaimeen
Allah ne masani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
25/Ramadan/1440 h.
30/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: