*FATAWOWI KAN ABUBUWAN DA BASA KARYA AZUMI.*
📝 Rubutawa: *Sheik Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*
1 Sa kwalli baya karya azumi. ibn taimiyya ibn usaimeen ibn Baz.
2 Diga Magani a ido, Baya karya azumi. Ibn taimiyya ibn usaimeen ibn Baz.
3 Maganin da ake sawa karkashin harshe baya karya azumi sai an Hadiye, Ibn usaimeen.
4 Diga magani a cikin kunne. Ibn taimiyya ibn usaimeen ibn Baz.
5 Maganin shakawa ga masu Asma. Saad Raslan.6 Allurar masu ciwon suger. Allajanatul daimah.
7 Allurar da ake yiwa mai ciwon hakori domin dauke radadi a cikin baki, bata karya azumi, Ibn Baz.
8 Shakar kamshin turarai, Ibn Baz ibn usaimeen.
9 Jambaki da mata suke sawa Ko muttaleta, domin bushewar lebe, Ibn Baz ,ibn usaimeen.
10 Daukan jini domin bincike, Ko gwaji, Ibn Baz ibn usaimeen.
11 Ninkaya da nutso a cikin ruwa, Ibn usaimeen.
12 Yin mafarki da rana a cikin watan Ramadan, Zaayi wanka amma azumi yananan idan ba da ganganci akayi ba, Ibn Baz ibn usaimeen.13 Yin aswaki, ba tare da hadiye ruwan ba, Ibn Baz ibn usaimeen.
14 Hadiye majina ko miyau, Ibn usaimeen.
15 Diga magani a hanci ba mai yawa ba, Ibn usaimeen.
16 shafa abinda zaisa lebe yayi laushi, Ibn usaimeen.
17 Zubar jinin habo, ko cirewar hakori, tare da fitar jini idan baa hadiye ba . Ibn usaimeen.
18 Yin amfani da makilin da burosh, amma kada a hadiye ruwan. Ibn usaimeen.
19 Dandana abinci. idan da bukata amma kada a hadiye.
20 Yin amai ko kumallo amma ba da ganganci ba. Ibn Baz ibn usaimeen.
21 Dukkan Allurar da ake yiwa mutum a cikin jijiya ko a akan fata , ko akan wata gaba ta musamman. Ibn Baz ibn usaimeen.
22 shinshina flower ko wani abu mai kamshi. Ibn usaimeen.
23 Mashakar iska ta oksigin. Saad kaslan.
24 kurar nan titi.
25 hayakin mota dana itace, banda hayakin sigari.
26 shakar doyi da wari na kashi ko mushe.27 mutum ya wayi gari da janaba, daga baya yayi wanka.
28 mutum ya sumbaci matar sa, amma yayi a hankali domin idan yayi zurfi zai karya azumi. sahihu fiqhusunnah.
29 Yin wanka da rana , saboda zafi. Sahihu fiqsunnah.
30 kurkurar baki da saka ruwa. Amma ayi a hankali kada ruwa ya wuce, Sahihu fiqhusunnah.
31 yin kaho ko bayar da gudunmawa ta jini, idan likita ya tabbatar ba zaa jigata ba . Sahihu fiqhusunnah.
32 cin abinci ko Shan ruwa da mantuwa . Sahihu fiqhusunnah.
33 Idan akayi wa mutum tilas yaci ko ya sha azumin sa bai karyeba. Sahihu fiqhusunnah.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Historia Corta*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: