*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
*HUKUNCIN WANDA YA YI ISTIMNÁ'I A YININ RAMADAN!*
TAMBAYA:
Assalamu alaikum, Mene hukuncin wanda yai istimnai da rana ana azumi?
AMSA:
Wa'alaikumus Salam, Istimná'i shi ne mutum ya yi wasa da al'aurarsa har ya fitar da maniyyi ba ta hanyar jimá'i ba. Yin hakan laifi ne babba, amma laifin yin sa a watan Ramadana yana qara girmama fiye da a sauran watanni.
An tambayi Allama Ibn Utsaimeen Rahimahullahu a game da wanda ya yi Istimná'i, shin kaffara ta wajaba a kansa? Sai Allama ya ba da amsa da cewa:"Idan mai azumi ya yi wasa da al'aurarsa (istimná'i) har ya fitar da maniyyi, to ya wajaba a kansa ya rama azumin wannan yini da ya yi istimná'i a ciki, amma babu kaffara a kansa, saboda kaffara ba ta wajaba sai idan jimá'i ne aka yi".
Duba Majmú'u Fataáwá na Ibn Uthaimeen 19/233.Kuma wanda ya sami kansa a wannan mugun aikin, bai halasta a gare shi ya ci abinci ko abinsha a wannan yinin saboda an ce azuminsa ya karye ba, wajibi ne a kansa ya kiyaye alfarmar watan ta hanyar kamewa daga ci ko sha duk da karyewan azumin nasa. Sannan ya wajaba a gare shi ya yi nadama tare da kyakkyawar tuba zuwa ga Allah, saboda wannan babban zunubai da ya aikata na Istimná'i da kuma karya azumi, kuma ya yawaita kyawawan ayyuka, saboda kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
12/Ramadan/1440 h.
17/05/2019 m.
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Conto*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: