*_HUKUNCIN FADIN "BALAA" A KARSHEN SURATU ATTIN_*
*Tambaya*
Assalam alaikum warahmatallah Malam dafatan kana lafiya amin. Malam akwai addua da akeyi a yayin da aka karanta Suratin Tin a karshen surar wato "Balaa nahanu ala zalika laminash shahideen". Ya ingancin wannan addua yake? Wassalam Allah ya kara lafiya.*Amsa*
Wa'alaikum assalam, akwai hadisin da Abu-dawud ya rawaito mai lamba ta (887) wanda ya tabbatar da hakan, saidai malaman hadisi sun raunana shi kamar Nawawy a cikin Al-majmu'ú 3/563.
Saidai wasu daga cikin malaman Malikiyya sun só fadin hakan in an karanta karshen Surar WATTIN, hakanan wasu a cikin Hanabila.Allah ne mafi sani.
04/08/2017
✍🏻
Amsawa:- *Dr. Jamilu Zarewa.*
YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: