*_INA CIKIN SADUWA DA MIJINA A RAMADHANA SAI ALFIJIR YA KETO!_*
*Tambaya*Assalamu alaikum Malam muna cikin saduwa da mijina a cikin wannan wata, sai muka ji kiran sallar asalatu, me ye hukuncin azuminmu?
*Amsa*
Wa'alaikumus Salam To 'yar'uwa mutukar kuna jin kiran sallar, kun maza da sauri, kun datse saduwar da kuke yi, to azumin ku yana nan, amma in har kuka ci gaba, da yi ko da na second daya ne, to azuminku ya karye, kuma za ku yi kaffara ku duka, idan kin yi masa biyayya, in kuma takura miki ya yi, to zai yi kaffara shi kadai.
Duba Almugni: 3\65.
Allah ne mafi sani.
05/9/1437
10/6/2016.*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.

YOU ARE READING
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*
Short Story*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA: