*NA QI YIN AZUMI SABODA KUNAMA TA HARBE NI DA DADDARE!*

237 5 0
                                    

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*NA QI YIN AZUMI SABODA KUNAMA TA HARBE NI DA DADDARE!*

TAMBAYA:

Assalami alaikum, malam da fatan an sha ruwa lafiya, ina da wata tambaya ce kamar haka: Mene ne hukuncin wanda ta ki yin azumi sakamakon kunama ta harbe ta da yamma aka kai ta asibiti suka yi mata  allura, sai washe gari ta ki yin azumi, kuma bayan harbin ta daina yin mata zafi?

AMSA:

Wa'alaikumus Salam, malaman Musulunci suna da fahimta guda biyu ga wanda ya karya azuminsa ba ta hanyar jimá'i ba, ga su kamar haka:

1. Matuqar ba zazzaɓin harbin kunamar nan ne ya hana ta yin azumi ba, kawai ta qi yi ne saboda sakaci, da fakewa da harbin kunamar can, to ta saɓa wa Allah da qin yin wannan azumi da ta yi, ta tuba zuwa ga Allah, kuma kaffara ta wajaba a kanta, tare da rama azumin da ta sha a fahimtar malaman da ke qiyasta hukuncin jimá'i da hukuncin karya azumi da gangan ba ta hanyar jimá'i ɗin ba a yinin Ramadana.

Kaffarar da ke kanta shi ne ciyar da miskinai sittin, ko ƴanta kuyanga (baiwa), ko yin azumi sittin a jere, tare da rama azumin ranar da aka sha, kamar yadda Ibn Abi Zaid ya faɗa a Risala, a Babus Siyam.

Idan kuwa harbin kunamar nan ya sabbaba mata zazzaɓin da zai iya hana ta yin azumi, sai ba ta sami damar yi ba, to wannan tana da uzuri na shan azumi, abin da ke kan ta shi ne ramuwa. Amma ta ji tsoron Allah, domin Allah ya san abin da kowa ya ɓoye a zuciyarsa, idan mutum ya yi qaryar ba shi da lafiya ya qi yin azumi Allah ya sani, kuma zai hukunta duk wanda ya yi hakan, saboda ba a isa a yi wa Allah wayau ba!

2. Amma a wurin malaman da suke da fahimtar kaffara ba ta hawa kan kowa sai wanda ya karya azuminsa ta hanyar jimá'i kaɗai, to abin da ke kanta shi ne rama azumin wannan yini kaɗai, tare da kyautata tuba zuwa ga Allah, ba tare da wata kaffara ba, saboda a fahimtarsu kaffara tana wajaba ne kaɗai ga mai azumin da ya yi jimá'i a yinin Ramadana, saboda shi ne nassi ya wajabta wa kaffara kaɗai qarara, ban da wanda ya karya azuminsa ta wata hanya ta daban.

Allah ne mafi sani.

*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍🏻
9/Ramadan/1440 h.
14/05/2019 m.

*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*Where stories live. Discover now